Tsaron ku shine babban fifikonmu – Gwamna Dauda ga masu yiwa Ƙasa hidima

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bai wa matasa masu yi wa ƙasa hidima da aka tura jihar tabbacin aniyar gwamnatin sa na tabbatar da tsaro da walwala da duk wani tallafi da ya kamata a yayin gudanar da ayyukansu na bautar ƙasa a jihar.

Gwamnan ya bayar da wannan tabbacin ne a wajen bikin rantsar da masu bautar Ƙasar watau ‘C’ 2024 stream 1 wanda aka gudanar a sansanin horar da masu yi wa ƙasa hidima na wucin gadi NYSC na jiha, dake cibiyar horar da Malamai UBEC da ke Gusau yau Juma’a.

Gwamna Dauda Lawal wanda ya samu wakilcin babban sakatare na ma’aikatar matasa da ci gaba Alhaji Nasiru Galadima a wajen taron ya bada tabbacin samar da duk wasu buƙatu da ake buƙata domin masu bautar Ƙasar su samu ingantacciyar walwala.

Ya yabawa jami’an NYSC na jihar da dukkan hukumomin da suka jajirce wajen jagorantar matasan masu yiwa Ƙasa hidima da aka tura jihar.

“Gwamnati na za ta ci gaba da haɗa gwiwa da hukumar masu yi wa ƙasa hidima domin tabbatar da cewa jihar ta samu alfanun wannan gagarumin shirin”. Gwamna Lawal ya bayyana

Gwamna Lawal ya buƙaci sabbin masu yi wa ƙasa hidima da aka tura jihar Zamfara da su ɗauki kowane ɓangare na kwasakwasan da muhimmanci tare da kula da laccocin da za a basu domin su samu ilimin zama jihar ta Zamfara.

A jawabinsa na buɗe taron, kodinetan NYSC na jihar Zamfara, Muhammad Lawan Ahmad ya buƙaci masu yiwa Ƙasa hidimar da su kasance jakadu nagari kuma su guji aikata duk wani nau’in laifi da zai iya ɓata musu suna a lokacin da suke yi wa ƙasa hidima a jihar.

By ukarofi