Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta gina makarantun firamare guda 44 da gyara wasu makarantun guda 51 tare da samar masu da tebura da kujeru na malamai da ɗalibai a faɗin jihar.
Gwamna Dikko Raɗɗa ya faɗi haka lokacin da yake jawabi kafin gabatar da kasafin kuɗin 2025 a zauren Majalisar Dokoki na jihar.
Yace gwamnati ta kashe wajan Naira biliyan 1.78 wajen waɗannan aikace aikace da ya shafi ilimin firamare a jihar.
Haka kuma Malam Dikko Raɗɗa ya bayyana cewa malaman gaba da firamare dubu 10 suka sami horo daban daban akan sanin makaman aiki ƙarƙashin shirin AGILE na bankin duniya.
Ya cigaba da cewa gwamnatin Jihar Katsina ta gina makarantun gaba da firamare guda 75 da horas da malaman makarantun su 5000 akan noman zamani.
Su ma ɗaliban makarantun sakandare guda 2000
su ka sami horo akan yadda ake haɗa ganyen shayi a kwalin sa.
Gwamnatin Katsina ta kuma gudanar da mayan gyare-gyare a makarantun sakandare na jeka ka dawo a garin Funtua, Jiƙamshi,Zango da Kabomo akan kuɗi Naira miliyan 452.
Haka kuma Dikko Raɗɗa ya bayyana cewa gwamnati ta kashe kuɗi rabin biliyan wajan gina ofisoshi da katangar sashin makwancin mata ‘yan makaranta a manyan makarantun jihar.
Duk dai a fannin ilimi, gwamna Raɗɗa ya ce, gwamnati ta fara aikin gina makarantun sakandare na zamani guda uku a shiyar Katsina, Funtua da Daura.
“Su waɗannan makarantu sakandare idan an kammala gina su, za su yi gogayya da kowace makarantar sakandare a duniya wajen bada ingantaccen ilimi”.malam Dikko Raɗɗa yayi Wannan alƙawarin.
Ya faɗawa Majilisar cewa wannan matakai da gwamnatin take ɗauka akan fannin ilimi,shine a rage cinkoso a azuzzuwa da kuma samar da wadatattun malamai,ƙarin yawan ɗalibai da zai samar da sakamako mai kyau.
A kasafin kuɗin na 2025 gwamnatin Katsina ta bai wa harkan ilimi kaso mai tsoka na Naira biliyan 95 wanda ya yi dai dai da kashi 14%.
