Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Rundunar sojin saman Nijeriya ta ce jiragen samanta sun kashe mayaƙan Boko Haram da dama a ranar 25 ga Oktoba a arin Bula Marwa a Borno.
Daraktan hulɗa da jama’a na rundunar, Iya Comodore, Olusola Akinboyewa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin a Abuja.
Akinboyewa ya ce sun gano Bula Marwa ne garin da Boko Haram suka taruwa, inda suka gano babura suna ta zirga-zirga, hakan ya sa aka aika jiragen sama yankin, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Nijeriya NAN ya ruwaito.
“Da isan jiragen, sai hoton da jiragen ya ɗauko ya tabbatar da taron ‘yan Boko Haram a saman babura 12, inda aka bibiyi baburan zuwa wani wuri da akwai ƙarin ‘yan ta’addan suke jiran zuwan su.
“Wannan ya sa jiragen suka yi ɓarin wuta a yankin, sannan daga baya jirgin ya hango ‘yan ta’addan suna sake dawowa yankin domin kwashe waɗanda suka raunata.
“Wannan ya sa jiragen suka koma, suka ƙara yin luguden wuta, inda a nan ma aka sake kashe wasu ‘yan ta’addan.”
Akinboyewa ya ce an sake ganin wasu tarin ‘yan Boko Haram sun taru a ƙarƙashin wata bishiya, inda nan ma jiragen suka ƙara bin su, suka musu ɓarin wuta.
