Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Rundunar Sojojin Nijeriya ta ce wasu dakarunta sun rasa rayukansu wajen ƙoƙarin daƙile wani mummunan harin da mayaƙan Boko Haram suka shirya kai wa a yankin Kashimri, cikin ƙaramar hukumar Bama, jihar Borno.
Harin, wanda aka yi ƙoƙarin kai wa a ranar 17 ga Oktoba 2025, rundunar ta ce sojojinta ƙarƙashin Operation Haɗin Kai su samu nasarar daƙile shi bayan da suka gano kuma suka lalata sansanonin ’yan bindigan da ke yankin.
A cikin sanarwar da rundunar ta fitar a shafinta na ɗ, kakakin rundunar, Laftanar Kanal Appolonia Anele, ta bayyana cewa sojojin sun fafata da ‘yan bingidar inda suka kashe da dama daga cikinsu, wasu kuma suka jikkata.
“Duk da nasarar da aka samu, kwamandan rundunar 202, Laftanar Kanal Aliyu Saidu Paiko, da wasu dakarun sojin sun rasa rayukansu a yayin fafatawar.” in ji sanarwar.
Sanarwar ta kuma ce “Waɗannan sojojin sun sadaukar da rayukansu ne don tabbatar da zaman lafiya da tsaron ƙasar, kuma rundunar za ta ci gaba da girmama tarihin jarumtar su.”
Rundunar ta bayyana cewa “Mutuwar waɗannan jami’an ta sake tunatar da ita muhimmancin ci gaba da yaki da ta’addanci har sai an tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Nijeriya baki ɗaya.”
Babban hafsan sojan ƙasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya mika ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka mutu.
Ya kuma tabbatar da cewa rundunar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen murkushe duk wani abu da ya shafi ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas da ƙasar baki ɗaya.
