Sojojin sama sun hallaka ‘yan ta’adda da Dama a dajin Sambisa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Rahotanni sun bayyana cewa rundunar sojin saman Nijeriya ta kashe wasu ‘yan ta’adda da dama bayan kai wani hari na musamman ta sama a yankin Yuwe da ke cikin dajin Sambisa a jihar Borno kamar yadda jaridar TheCable ta wallafa.

Majiyoyin soji sun shaida wa wata kafar yada labarai mai bibiyar yaki da ta’addanci a yankin Tafkin Chadi cewa an kai harin ne da yammacin ranar Lahadi da misalin karfe 5:45.

An ce harin ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da kuma sa ido da aka yi, wanda ya tabbatar da cewa ‘yan ta’adda na ci gaba da zirga-zirga a yankin, tare da kafa sansanoni masu karfi ciki har da ramukan buya.

Rahoton ya ce da isar jiragen yakin a wurin, matukan jiragen sun gano wuraren da aka nufa tare da kai musu farmaki da makamai masu inganci.

Majiyoyin tsaro sun ce harin ya lalata wuraren ajiyar kayayyakin ‘yan ta’adda da dama, ciki har da matsugunansu da maboyarsu, yayin da aka kashe wasu daga cikinsu.

An bayyana cewa wannan hari na daga cikin ci gaba da hare-haren hadin gwiwa ta sama da kasa da ake yi domin rage karfin ‘yan ta’adda, katse hanyoyin samun kayayyaki da kuma hana su ‘yancin motsi a yankunan da ake gudanar da ayyuka.

Mahukunta sun rufe shagunan siyar da magani 598 a Kaduna, sun yi kamen wasu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Hukumar kula da fannin magunguna ta Nijeriya (PCN) ta rufe shaguna 598 da kama wasu masu sayar da magungunan biyu Kaduna a yayin wani samame na daƙile shan miyagun ƙwayoyi da amfani da magunguna ba bisa ƙa’ida ba.

Shugaban hukumar PCN, Suleiman Chiroma, ne ya bayyana haka a yayin da yake magana da manema labarai a ranar Juma’a a Kaduna.

Mista Chiroma ya ce, an kai samamen ne a ranar Litinin a ƙananan hukumomi a Kaduna ta Arewa da Kaduna ta Kudu da Zariya da Makarfi da Kudan da Igabi da Chikun da Sabon Gari da Giwa da Ikara.

Ya kuma ce sun kai ziyara shaguna 828 a yayin samame da suka fito na kwanaki 4 da suka haɗa shagunan sai da magunguna da waɗanda ba sisi da lasisi.

Ya kuma ce an kama masu sayar da magunguna su biyu saboda karya dokar hukumar.

Ya ce kaso 9% na shagunan da suka duba suka gudanar da ayyukansu ne ba bisa ƙa’ida ba, wanda hakan ke nuna an samu ci gaba a yadda ake bin dokokin ƙungiyar.

Ya ƙara da cewa kaso 28 na shagunan magunguna suna bin doka a yayin da kaso 45% na manyan shaguna da kaso 28 na shagunan sayar da magunguna sun cika dukkan ƙa’idoji.

“Shagunan da aka rufe mafi yawa sun haɗa da waɗanda ba su da lasisi da gudanar da ayyukansu ba bisa ƙa’ida ba da rashin zuba magungunan da suka dace da masu haramtattun ayyuka da wasu da suka ƙi barin masu bincike duba shagunansu da sauransu,” ya faɗa.

A yayin da yake ƙarin haske, ya ce sun kai samamen ne da nufin gano magunguna masu illa da haramtattun ayyuka da ke barazana ga ingancein magunguna da rashin lasisi da sauransu.

Ya ƙara da cewa wannan mataki wani ɓangare ne na yunƙurin da take na kawo ƙarshen magunguna da ba su da inganci da jabun magunguna da nufin kare lafiyar al’umma.

Da yake bayani a kan hukumar, shugaban ya ce an kafa hukumar bisa doka ta 31 ta shekarar 2022 domin sa ido kan ilimin magunguna da horaswa da gudanar da harkar magunguna ciki har da masu sayar da magungunan.

Mista Chiroma ya ce, hukumar an ɗora mata alhakin tabbatar da an bi dokokin magunguna domin tabbatar da an bi tsarin da doka ta tanada na samar da magunguna da ko shigo da su.

Ya ce dokokin na ƙoƙarin tabbtar da killace magungunan yadda ya kamata da kare inganci da lasisi da tasirin magungunan a tsarin harkokin magunguna.

Ya ƙara da cewa suna ƙoƙarin rage yawan waɗanda ba su da ƙwarewa da rashin wuraren ajiyar magunguna da yaƙi da jabun magunguna da marasa inganci.

A cewarsa, matakin da suka ɗauka ya yi daidai da shirin shugaba Tinubu na inganta lafiya a ƙarƙashin shirin sabunta fatan ‘yan Nijeriya.

Ya kuma ce kawo gyaran na cikin matakan da ministan lafiya da walwalar jama’a, Muhammad Pate, tare da taimakon rajistara na PCN, Ibrahim Ahmed.

Mista Chiroma ya ce, babban burinsu shi ne samun magunguna masu inganci.

Sai dai ya koka game da yadda masu sa ido suka bankaɗo marasa bin ƙa’idojin hukumar da suka haɗa da masu rubuta wa mutane magunguna da sauransu.

Ya yi gargaɗin cewa irin waɗannan abubuwa barazana ce ga lafiyar al’umma inda ya ba da tabbacin cewa hukumar za ta ci gaba da tsaurara matakai domin tabbatar da masu ƙwarewa ne kaɗai suke harkar magunguna da nufin tabbatar da ingantaccen magunguna sun kai ga al’umma.

Ya yi kira ga al’umma da su riƙa sayen magunguna a wuraren da suke da shaidar lasisi sayar da magunguna tare da yaba wa al’ummar Kaduna kan irin haɗin kan da suka ba su.

Okebukola ya bayyana gamsuwa kan yadda sakamakon samun gurbin karatu ke ƙara inganta ga masu nakasa.

By ukarofi