Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Akalla ɗalibai 536 masu nakasar gani ne su ka rubuta jarabawar shiga makarantun gaba da sakandare ta 2026 (UTME), tare da sauran masu bukata ta musamman a fadin Nijeriya.
Shugaban Kwamitin Daidaiton Dama na JAMB (JEOG), Farfesa Emeritus Peter Okebukola, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke ganawa da manema labarai a ranar Litinin a Abuja, a lokacin kaddamar da zaman jarabawar musamman.
Ya ce an shirya gudanar da jarabawar ga ɗalibai 536 a cibiyoyi 11 da aka ware a fadin ƙasar nan, tare da tanade-tanade na musamman da suka dace da bukatunsu.
Tun daga shekarar 2017, JAMB ta hannun JEOG na bayar da tallafi iri-iri, ciki har da masauki kyauta ga daliban da masu rakiyarsu, abinci, tallafin sufuri da kuma kayan jarabawa na musamman.
Dangane da rabon daliban, Okebukola ya ce Kano ce ke kan gaba da ɗalibai 136, sai Lagos da 95, yayin da Abuja ke da 46.
Sauran cibiyoyin sun haɗa da Ado-Ekiti, Bauchi, Benin, Enugu, Kebbi, Oyo, Jos da Yola, inda kwararrun malamai ke sa ido, da dama daga cikinsu tsofaffin shugabannin jami’o’i ne.
