Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya taya sabon ministan gidaje da raye birane Injiniya Muttaƙa Rabe Darma murnar samun muƙamin minista a gwamnatin Tinubu
Gwamna Raɗɗa ya yaba da ƙoƙarin shugaban ƙasa wajen cigaban ƙasa.
Ya bayyana ƙwarin gwiwarsa kan cewa Dakta Muttaƙa Darma yana da ƙwarewa da zai iya kawo ci gaba a fannin gidaje da raya birane a matakin ƙasa.
Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa wannan naɗin wata alama ce ta amincewa da ƙwarewa, jajircewa da kuma halayen shugabanci na Dakta Darma.
“Mun yi alfahari da ganin ɗaya daga cikin ‘ya’yanmu ya samu wannan muƙami mai muhimmanci a matakin ƙasa, Dakta Muttaƙa Rabe Darma yana da gaskiya da hangen nesa da zai kawo wa ma’aikatar. Ba ni da shakka zai yi wa ƙasa hidima da kima,” in ji Gwamnan.
