Su waye tsoffin gwamnonin masu son fafatawa a neman kujerar shugabancin APC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tun bayan kammala zabukan shugabannin babbar jam’iyyar hammaya ta PDP a Nijeriya hankula suka karkata kan jam’iyya mai mulki, APC, domin ganin yaddaa za ta kaya.
Hakan ba ya rasa nasaba da ƙurar da rikicin da ya ɓarke a wasu jihohi bayan zaɓukan da jam’iyyar ta APC ta gudanar kamar yadda aka gani a jihohi irin su Kano da Zamfara da Kwara da dai sauransu.

Sai dai a yayin da jam’iyyar take fama da matsalolin da suka faru sakamakon zaɓen cikin gida, a gefe guda kuma tuni wasu manyan ‘yan siyasa suka soma fafutikar ganin sun samu shugabancin ta a mataki na ƙasa.

Kawo yanzu dai mutanen da aka fi jin amonsu sun haɗa da wasu tsofaffin gwamnoni huɗu waɗanda suka fito daga ɓangaren Arewaci. Hakan na da alaƙa da hasashen da wasu ‘yan jam’iyyar masana harkokin siyasa suke yi cewa ɗan takarar shugabancin ƙasar na APC za zai fito ne daga Kudancin ƙasar. Masu nazari kan harkokin siyasa na ganin cewa APC na buƙatar ƙwararre, gogagge kuma jajurtaccen shugaba domin ɗinke ɓarakar da ke cikin jam’iyyar.

Gwamnonin sun haɗar da tsohon gwamnan Jihar Borno, Ali Modu Sheriff da tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdul’aziz Abubakar Yari da George Akume tsohon gwamnan Jihar Benuwai da kuma Umaru Tanko Al-Makura, tsohon gwamnan Jihar Nasarawa.

Bari mu ɗa  waiwayi dukan waɗannan ‘yan siyasa a taƙaice:

Abdul’aziz Abubakar Yari:
Abdul’aziz Abubakar Yari, mai shekara 53, gogaggen ɗan siyasa ne, wanda sau biyu yana zama gwamnan Jihar Zamfara. Ya zama gwamnan jihar a ranar 29 ga watan Mayun 2011, ya kuma kammala wa’adinsa na biyu a 2019. Ya tava riqe shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewacin Nijeriya, kafin nan ya tava riƙe shugaban jam’iyyar ANPP a jihar Zamfara.

Yari

Bayan kammala wa’adin mulkinsa na gwamna, Abdul’aziz Yari ya yi takarar Sanata a zaven shekarar 2019 kuma ya ci, amma rikicin cikin gida na jam’iyyar su ta APC ya sa Kotun Ƙolin Nijeriya ta ruguza zaɓen ta bai wa PDP nasara. Sai dai Abdul’aziz Yari ya ci gaba da taka rawa a bayan fage a jam’iyyar.

Ali Modu Sheriff:
Ali Modu Sheriff fitaccen ɗan siyasa ne da ya fito daga Jihar Barno da ke Arewa maso Gabashin Nijeriya. Yana da shekara 66 a duniya. Modu Sheriff ya riƙe muƙaman siyasa daban-daban. Tun a jamhuriya ta uku Modu Sherrif ya riƙe muƙamin Sanata mai wakiltar Barno ta Tsakiya ƙarƙashin jam’iyyar UNCP lokacin mulkin Sani Abacha. A 1999 lokacin jamhuriya ta huɗu an ƙara zaɓar sa a wannan matsayi ƙarƙashin jam’iyyar ANPP.

Ali Modu Sheriff

A 2003, an zaɓi Modu Sherrif a matsayin gwamnan Jihar Barno ƙarƙashin ANPP, an sake zaɓensa a 2007. Fitaccen ɗan siyasar ya sauya jam’iyyu da dama, ya fara siyasar sa ne a ƙarƙashin jam’iyyar ANPP a 2003, har zuwa 2013 amma daga bisani gamayyar wasu jam’iyyu da suka haɗa da CPC da ACN da kuma ita ANPP ɗin suka dunƙule suka kafa APC, inda shi ma ya koma cikinta a 2014.

Daga wannan shekarar ya koma PDP har zuwa 2018, inda a PDP ya riqe muƙamin shugaban kwamitin zaɓen shugabannin jam’iyyar a 2016. Ya samu kansa a cikin turka-turkar shugabancin jam’iyyar PDP a 2017, sai dai daga bisani Kotun Ɗaukaka ƙara da ke jihar Ribas ta yi watsi da ikirarinsa na shugabancin jam’iyyar.

George Akume:
Akume babban ɗan siyasa ne daga Jihar Benuwai da ke Arewa ta Tsakiyar Nijeriya, wanda yake da shekara 67. Yanzu haka yana riqe da muqamin Ministan Ayyuka na musamman da kuma harkoki tsakanin vangarorin gwamnati.

George Akume

Ya riƙe matsayin shugaban marasa rinjaye na majalisar dattijan Nijeriya a 2011 zuwa da 2015. An zaɓe shi a matsayin Sanata mai wakiltar Benuwai ta Arewa maso Yamma a 2011 har zuwa 2015 da aka ƙara zaɓarsa, amma a 2019 sai ya gaza kai bantensa, inda ya sha kashi a hannun ɗan takarar jam’iyyar APC.

Gabanin haka a 1999 lokacin da za a fara jamhuriyya ta hudu, ya fito takarar gwamnan kuma ya yi nasara, inda ya kwashe shekara takwas a kan mulki. Bayan ya faɗi zave ne Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da sunansa cikin waɗanda za a bai wa muƙami, an kuma ba shi matsayin Ministan Ayyuka na musamman da kuma harkoki tsakanin vangarorin gwamnati.

Umaru Tanko Al-Makura:
Al-Makura tsohon ɗan gwagwarmayar siyasa ne domin kuwa tun a 1980 ya riƙe matsayin shugaban matasa na jam’iyyar NPN lokacin ƙarƙashin tsohuwar Jihar Filato. Bayan haka, ya riƙe muƙamai da dama na siyasa da wakilci.

Tanko Al-Mamura

Yana cikin jiga-jigan da suka kafa jam’iyyar PDP a 1998. Ya zama gwamnan Jihar Nasarawa har sau biyu, inda aka zave shi a 2011 ƙarƙashin jam’iyyar CPC, sai dai daga bisani da CPC ta dunƙule cikin jam’iyyun da suka kafa APC inda ya ci gaba da jan zarensa a cikin jam’iyyar.

Masana harkokin siyasa dai na ganin za a fafata sosai wajen zaɓen shugaban jam’iyyar ta APC, kuma da alama an kama hanyar zaɓen bayan da shugaban ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar kuma gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Bagudu, ya sanar da cewa a watan Fabrairun 2022 za a gudanar da babban taron jam’iyyar.