Sufeto-Janar ya maye gurbin Abba Kyari da DCP Disu

Sufeto-Janar na ‘yan sandan Nijeriya, Usman Alkali Baba, ya naɗa DCP Tunji Disu a matsayin sabon shugaban sahen Intelligence Response Team (IRT) na rundunar.

Disu ya gaji Abba Kyari wanda a kwanan nan aka dakatar da shi daga aiki bisa zargin rashawa da hukumar FBI ta ƙasar Amurka ta yi masa.

Kyari wanda shi ma Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda ne, an zarge shi da karɓar cin hanci daga hannun hamshaƙin mai kuɗin nan wanda ya gawurta wajen damfara, wato Abbas Ramon wanda aka fi sani da Hushpuppi.

Mai magana da yawun rundunar, Frank Mba, shi ne ya bayyana naɗin Disu cikin sanarwar da ya fiitar ran Litinin.

Mba ya ce hukumar rundunar ta ɗauki matakin naɗa Disu ne domin cike giɓin da aka samu a sashen IRT don bai wa sashen damar ci gaba da gudanar da ayyukansa yadda ya saba.

Ya ƙara da cewa, Sufeto-Janar ya hori sabon shugaban na sashen IRT da ya yi aiki da ƙwarewa wajen jan ragamar sashen. Tare da bai wa ‘yan ƙasa tabbacin sashen zai ci gaba da gudanar da harkokinsa daidai da dokokin ƙasa.

Kafin naɗin nasa, Disu ya shugabanci sashen RRS na rundunar a Legas, kuma Mataimakin Kwamishina a sashen ayyuka a hedikwatar rundunar da ke Abuja.