‘Yar Shekarau ta rasu a Dubai

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Bayanan da Manhaja ta samu sun nuna Allah Ya yi wa ‘yar Sanata Ibrahim Shekarau rasuwa a Dubai a Litinin da ta gabata.

Mai bai wa Shekarau shawara kan harkokin yaɗa labarai, Dakta Sule Yau Sule, shi ne ya bayyana haka cikin sanarwar da ya fitar ran Litinin.

Sanarwar ta nuna marigayiyar wadda ‘yar wattani biyar ce da haihuwa, an kai ta jinya a wata asibitin Dubai da ke ƙasar Larabawa inda a can Allah Ya karɓi ranta, kuma tuni aka yi mata jana’iza daidai da karantarwar addinin Musulunci.

Shekarau shi ne sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawan Nijeriya, tsohon gwamnan Kano na wa’adi biyu, kuma tsohon Ministan Ilimi.