Allah Ya yi wa tsohon Minista, Malami rasuwa

Daga WAKILINMU

Tsohon Ministan Harkokin Gona, Dr. Malami Buwai ya rasu bayan ya yi fama da rashin lafiya.

Malami ya yi Ministan Gona ne a zamanin mulkin marigayi Janar Sani Abacha a 1994.

Marigayin ya rasu ne a jiya Litinin da rana a Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

Ya rasu yana da shekara 76, inda ya bar mata ɗaya, ‘ya’ya 15 da kuma jikoki 10. Daga cikin ‘ya’yan nasa, har da ɗan kasuwar nan Alhaji Shehu Malami.

An yi wa marigayin jana’iza ne a maƙabartar Gusau bayan da Babban Limamin Masarautar Gusau, Liman Ɗan-Alhaji Sambo ya jagoranci yi masa sallah.

Janazar ta samu mahalarta da dama ciki har da Gwamnan Zamfara, Bello Muhammad Matawalle, da mataimakinsa Mahadi Aliyu da sauransu.

Tarihin marigayin ya nuna an haife shi ne a 1945. Kuma kafin rasuwarsa ɗan Ƙungiyar Manoma ta Ƙasa (AFAN) reshen Gusau ne.