Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta yi ƙwaƙƙwaran bincike kan sulhu da da ake yi da ‘yan bindiga a jihar.
Rahotonni sun bayyana yadda wata tawaga ta Gwamnatin Tarayya take gudanar da zaman sulhu da ‘yan bindiga a Zamfara, ba tare da sanin Gwamnatin Jihar ba.
A wata sanarwa wacce mai magana da yawun Gwamna Lawal, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a ranar litinin, gwamnatin ta Zamfara ta yi Allah wadai da tawagar ta Gwamnatin Tarayya wacce take jagorantar wannan sulhu, tare da alhinin cewa ko tuntuɓar gwamnatin jihar ba a yi ba.
Sanarwar ta ƙara da cewa, Gwamna Lawal ya nemi Gwamnatin Tarayya da ta yi bincike tare da yin bayani kan wannan sulhu, domin ya saɓa da matsayar da gwamnatinsa ta ɗauka tun farko.
Ya ce: “Gwamna Dauda Lawal yana neman ƙarin bayani daga Gwamnatin Tarayya kan sulhun da wasu waɗanda suka kira kansu wakilanta suke aiwatarwa a Jihar Zamfara.
“Gwamnatin Jihar Zamfara ta samu rahotanni cewa waɗannan wakilai na Gwamnatin Tarayya sun yi zaman sulhu da ‘yan bindiga a Birnin Magaji, Maradun, Mun Haye, Ajah, Bawo, da kuma Bagege.
“Sanin kowa ne, gwamnatocin baya da suka gabata a Jihar Zamfara sun jaraba yin sulhu da ‘yan bindiga, kuma abin bai haifar da ɗa mai id oba.
“A dalilin haka ne gwamnatin Zamfara ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal ta bayyana matsayarta tun farko – cewa, babu ranar yin sulhu da ‘yan bindiga.
“Wannan matsaya ce da aka ɗauka domin tabbatar da an yaƙi wannan ɓarna gabaɗayanta. Kuma muna ganin nasarorin da ake samu ba ta hanyar yin sulhu ɗin ba. Muna kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta dakatar da wannan sulhu, domin ba alheri ba ne ga al’umman Jihar Zamfara.”
