Masu garkuwa sun ɗauki salon ɗauki-ɗaiɗai a Kebbi 

Daga JAMIL GULMA a Kebbi 

Masu garkuwa da mutane sun ɗauki sabon salo a waɗansu sassan Jihar Kebbi, inda yanzu a maimakon kai hari da suke yi a baya a cikin ayarin babura masu yawa, sun ɗauki salon ɗauki-ɗaiɗai, inda suke shiga cikin gari da tsakar dare su ɗauki mutum ɗaya ko biyu zuwa biyar maimakon ayarin mutane.

Yankin ƙananan hukumomin Koko/Besse, Bagudo da Maiyama dai yanzu a nan ne waɗannan mutanen ke cin karensu ba babbaka duk da irin ƙoƙarin da hukumomin tsaro da ’yan sa-kai ke yi.

A cikin daren ranar Larabar da ta gabata waɗannan mutanen sun shiga garin Dutsin Mari suka yi awon-gaba da wani mutum mai suna Alhaji Haro.

Wani daga cikin mazauna garin na Dutsin Mari da bai so a bayyana sunansa ba saboda dalilin tsaro, ya bayyana cewa, ya ji wani motsin da bai yarda da shi ba a cikin daren sai dai bai haska fitila ba kuma bai ga kowa ba, amma dai hankalinsa ya tashi, saboda haka sai ya shiga gidansa ya vuya. Sai da safe bayan ya fito ya ke jin labarin abinda ya faru.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Mulki ta Koko/Besse, Honarabul Yahaya  Bello Koko (Sarkin Gabas), ya isa garin na Dutsin Mari tare da shugaban rundunar hukumar ‘yan sanda na ƙaramar hukumar mulkin da sauran jami’an tsaro, inda ya jajenta wa iyalan Alhaji Haro tare da tabbatar musu da cewa in sha Allahu gwamnati ba za ta yi qasa a gwiwa ba wajen ɗaukar matakin yaqi da vata-gari.

“Wannan aikin ba na hukuma kaɗai ba ne, kowa yana da rawar da zai iya takawa wajen wanzar da tsaro ta hanyar kai rahotanni ga hukumomin da ke kusa da su kan duk abinda ba su yarda da shi ba,” inji Shugaban Ƙaramar Hukumar.

Sarkin Gabas ya kai wa iyalansa tallafin abinci da kuɗi tare da miƙa saƙon jajen Gwamnan Jihar Kebbi, Malam Nasir Idris Ƙauran Gwandu.

Wakilin Blueprint Manhaja ya nemi jin ta bakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kebbi, sai dai Kakakin Rundunar, SP Nafi’u Abubakar, bai ɗauki waya ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.