Ta halaka saurayinta kan zargin cin amana

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wata mata mai suna Augustina Mowari ta caka wa saurayinta mai suna Michael Ikuedowoni almakashi bisa zargin sa da cin amanarta a soyayyarsu inda a sanadiyyar haka ya haɗu da ajalinsa.

Lamarin ya auku ne a Ƙaramar Okitipupa dake jihar Ogun a ƙarshen makon da ya gabata.

Augustina ta caka masa almakashin ne a lokacin da suka fara cacar baki a tsakaninsu a gidan da suke zaune, kamar yadda wasu muryoyi suka bayyana.

Wani abokin mamacin na kusa da ya nemi a sakaye sunansa ya ce suna fara rikici ne a lokacin Augustina ta fara zargin Ikuedowoni da kwana da waɗannsu mata a waje.

Ya ce, da fari an kai Michael wani asibiti da ke kusa da inda abin ya faru, sannan aka sallame shi bayan yi masa wasu allurori da rubuta masa wasu magunguna.

Baya ga haka ne ƙafarsa ta fara kumbura inda aka mayar da sho asibitin kana daga bisani ya cika.

A lokacin da ya ke magana mgame da lamarin, Kakakin ƴan sandan jihar, DSP Olayinka Ayanlade ya ce an kama wanda ake zargin kuma ana gudanar da bincike akanta.

By Babaji