Hukumar CAC ta ba kamfanoni 100,000 da ba sa aiki wata uku ko ta soke su

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Tattara bayanan Masana’antu Masu zaman kansu (CAC) ta yi barazanar soke rajistar kamfanoni guda 100,000 bisa ɗaukar tsawon lokaci ba tare da gudanar da harkokinsu ba a ƙarƙashin dokokin da suka shafe su ta CAMA.

Hakan wani yunƙuri ne na tsaftace ayyukan hukumar da tabbatar da kamfanonin da ke aiki ne kaɗai ke da rajista a wajenta.

Sannan, matakin zai taimaka wajen inganta harkar mallakar kamfanoni da jagorancinsu don tabbatar da kiyaye tsare-tsaren yaƙi da badaƙalar kuɗaɗe.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta bayyana kamfanonin a matsayin waɗanda ba sa gudanar da kasuwanci ko harkokinsu na tsawon aƙalla shekaru 10 ko kuma suka gaza cike ƙa’idodin da ta gindaya musu.

Akan haka ne ta ba su kwanaki 90 na su dawo da ayyukansa yadda ya dace ko kuma ta soke su daga cikin waɗanda ta yi wa rajista.

Kazalika, CAC ta ce wajibi ne su gaggauta biyan kuɗaɗen da ake bin su na shekara-shekara, sannan su bada bayanai akan haka ta adireshinta na Imel kamar haka: [email protected]

By Babaji