Ambaliyar Adamawa: Adadin wanda suka rasu ya kai 23

Spread the love

Daga USMAN KAROFI a Abuja

Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya tabbatar da mutuwar mutane 23 sakamakon ambaliya da ta faru a ranar Lahadi a wasu sassan jihar. Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin bayan isa filin jirgin sama na Yola da misalin ƙarfe 1:45 na rana, inda ya wuce kai tsaye zuwa yankunan da ambaliyar ta fi shafa a ƙaramar hukumar Yola ta Kudu.

A wata ziyarar ta’aziyya da ya kai wa wadanda suka rasa muhallansu a sansanin wucin gadi da ke makarantar firamare ta Yelewa, Gwamna Fintiri ya nuna alhini matuka tare da tabbatar musu da cewa gwamnatin jihar za ta kawo ɗauki cikin gaggawa don rage musu raɗaɗin wannan ibtila’i.

Fintiri ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta kafa kwamiti na musamman tare da haɗin gwiwar hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Adamawa (ADSEMA) da ta ƙasa (NEMA) domin gudanar da cikakken bincike kan girman ɓarnar da ambaliyar ta haifar.

Gwamnan ya kuma yi kira ga al’umma da su kasance masu juriya da fahimta yayin da gwamnati ke ɗaukar matakan bayar da tallafi ga duk waɗanda wannan musiba ta rutsa da su.

By ukarofi