Ta hannun gwamnati kaɗai za a shigo da rigakafin korona, cewar Mamora

Daga AISHA ASAS

Gwamnatin Tarayya ta ce ba ta yarda ‘yan kasuwa su shigo da allurar rigakafin cutar korona ba, tare da cewa dole dukkan rigakafin da za a shigo da su ya kasance ta hannun gwamnati.

Ƙaramin Ministan Lafiya, Olorunnimbe Mamora ya faɗi haka ran Talata a Abuja.
Ministan ya ce ‘yan Nijeriya masu bukatar a yi musu rigakafin korona sai su yi rajista a shafin intanet na Hukumar Kula da Lafiaya a Matakin Farko.

Mamora ya ce a halin yanzu ba a yarda ‘yan kasuwa su soma harkar shigo da allurar rigakafin korona ba. Ya ce gwamnati ba za ta ɗauki alhakin duk wani abu da ya biyo baya baidan aka shigo da maganin ta baya.

Tun bayan da gwamnati ta ƙaddamar da allurar rigakafin korona, tuni jihohi suka soma karɓar kasonsu daga Gwamnatin Tarayya, inda jihar Ogun ta zama jiha ta tafarko da ta karɓi nata kason. Haka ma Barno, Kano, Legas da sauransu sun karɓi nasu.