Ta kashe ‘yar uwarta akan bashin N800 A Ondo

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wata ‘yar kasuwa a Akure, babban birnin jihar Ondo, Bosede Iluyemi, ta kashe ƙanwarta mai suna Omowumi Tewogboye kan bashin Naira 800.

Manhaja ta ruwaito cewa Bosede ta buƙaci a biya ta kuɗin tumatur da barkono Omowumi da ta saya a kan bashi.

Lamarin ya rikiɗe zuwa tashin hankali lokacin da ake zargin Bosede ta riƙe kayan Omowumi, wanda hakan ya sa ta faɗi ta kuma samu munanan raunuka.

Nan take aka garzaya da Omowumi asibitin da ke kusa, amma abin takaici, an tabbatar da mutuwarta da isar ta.

Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo ta yi gaggawar mayar da martani, inda ta cafke Bosede tare da tsare ta.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Olusola Ayanlade, ya bayyana cewa a halin yanzu ana gudanar da bincike kan lamarin, inda ya tabbatar da cewa za a yi adalci.

By ukarofi