Tabbas makomar Kannywood mai kyau ce – Momoh 

Spread the love

“Bayar da gudunmawa ga haɓakar adabin Hausa abu ne da na yi alfahari da shi”

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano 

Aminu Aliyu Shariff Momoh, wanda da aka fi sani da Aminu Momoh na ɗaya daga cikin manyan jarumai kuma fitattu da suka bayar da gagarumar gudunmawa a masana’antar fim ta Kannywood, domin Momoh ya kasance a Kannywood tun shekaru 24 da suka gabata. Don haka za mu iya cewa, ya kasance daga cikin ɗaiɗaikun jaruman da ba sa tsufa a masana’antar Kannywood. 

A wannan makon, shafin Nishaɗi na jaridar Blueprint Manhaja ya tattauna da jarumin don samar wa masu karatu wasu daga cikin tambayoyin da suke da ga jarumin, wanda ya ga jiya, kuma yake ganin yau.

A wannan tattaunawar wadda ya yi da wakilinmu a Kano, Ibrahim Hamisu, ya bayyana tarihinsa, nasarorinsa da muhimman bayanai da ya kamata ku sani game da jarumin. Don haka, ku biyo mu don jin yadda tattaunawar ta kasance:

MANHAJA: Da farko muna maka barka da kasancewa da mu a wannan jarida ta Manhaja. Aminu Momoh, Bari mu fara da tarihin rayuwarka. 

AMINU MOMOH: Ina farin ciki da kasancewa tare da ku. An haife ni a ranar 17 ga Fabrairu, 1977, a Jihar Kano, Nijeriya. Na yi nazarin kimiyyar siyasa a Jami’ar Bayero, Kano, kuma daga baya kuma na samu shaidar karatun daban-daban a fannin fim daga cibiyoyin ilimi daban-daban.

Ta yaya tafiyarka ta cikin Kannywood ta samo asali?

Na fara ne a matsayin marubucin labarin fim, wato ‘Scriptwriter’ a Turance, inda na fara a kamfanin Ibrahimawa na tsawon lokaci, daga nan sai na zama mai shiryawa, sai darakta sai kuma na zama jarumi, a fim ɗin ‘Uƙuba’ na fara aktin a shekarar 2001, inda daga nan ne na sami sunan Momoh.

Baya ga ƙwarewa da ka yi a ɓangaren fim, kana da ƙwarewa a harkar yaɗa labarai da yanar gizo. Ko za ka yi mana ƙarin bayani a kan haka?

Haka ne, bayan yin fim, na kafa kafar sadarwa mai suna Madubi wanda ya zama mujallar fim. Sannan sai na tafi gidan talabijin inda na zama ɗaya daga cikin ma’aikatan Arewa24, inda na zama mai gabatar da shirin nan mai suna Kundin Kannywood.

Ka taka muhimmiyar rawa a masana’antar fim ta Kannywood. Za mu so ka yi mana bayani a kai ?

A tsawon shekaru, na sami damar taka muhimmiyar rawa a Kannywood, wanda hakan ya sa na sami kyaututtuka daban-daban da suka daɗa da; Jarumin Jarumai a tarukan karramawa mahimmanci a matsayi a cikin manyan toshewar Kannywood. Aikina ya sami yabo sosai mai martaba mai daraja, kamar mafi kyawun wasan kwaikwayo a lambobin yabo na Arewa Film Awards, a shekara ta 2001 da fim cin ‘Ukuba’; da jarumin jarumai na Gamji Awards, a shekara ta 2005, tare da fim din ‘ƙauna’, sai kyautar Jarumin Jarumai na Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano shekarar 2010, da fim ɗin ‘Makashi’, lambar yabo ta Jarumin Jarumai ta Afro-Hollywood Award (ɓangren finafinanan Hausa) a shekarar 2009, da fim ɗin ‘Duniyar Sama’. Sai Jarumin Jarumai na People Entertainment Awards a shekarar 2013, da sauransu.

A bayyane yake ka taka muhimmiyar rawa sosai a cigaban masanantar Kannywood. Mene ne sirrin?

Abin da na fi so dama shi ne bada labarin fim da kuma sinema na Hausa na ci gaba da tafiya. Na yi imani cewa da ƙarfin finafinai za a iya ilmantarwa da fadakarwa da kuma alkinta al’adunmu. Bayar da gudunmawa ga haɓakar adabin Hausa da kuma sinema wani abu ne da na yi alfahari da shi.

Muna godiya da ka ba mu lokacin ka. Daga ƙarshe mene ne saƙonka ga masoyanka da abokanen sana’arka ƴan masana’antar Kannywood? 

Da farko ina godiya ga Blueprint Manhaja.

Ga matasa masu tasowa kuwa ina cewa; ku cigaba da dagewa da koyo sannu a hankali za a kai ga babban mataki, masana’antar Kannywood tana da damarmaki da yawa, a yanzu da kuma nan gaba, tabbas makomarta mai kyau ce.

Ina godiya.

By ukarofi