Mu taimaka wa jami’an tsaro gano maɓoyar ’yan ta’adda

Spread the love

Haɗin gwiwar jami’an ’yan sanda da jama’ar gari ko farar hula wajen inganta aikin samar da tsaro a cikin al’umma ya fara ne tun a shekarar 2004 sakamakon yadda aikata laifuka ya yi tsamari a tsakanin al’umma tun a wancan lokacin. Don haka aka ƙirƙiro da rundunar ’yan banga, waɗanda suke zaɓaɓɓun mutane ne daga cikin al’umma da suka amince su ba da lokacin su da rayuwarsu, don samar da kariya a cikin al’ummarsu. Ba wai don sun zama ‘yan sanda ba, amma saboda kusancin su da jama’a, za su iya riga jami’an tsaro saurin samun bayanai da gano maɓoyar ɓata gari da duk wasu lunguna da ake aikata rashin gaskiya, da kuma kai ɗaukin gaggawa, kafin jami’an tsaro su kai ɗauki daga baya. 

Wannan ƙawance tsakanin amintattun cikin jama’a da jami’an tsaro yana da muhimmanci sosai wajen inganta tsaro, samar da yarda a tsakanin jama’a da hukuma, da haɗa ƙarfi waje guda don a yaƙi masu aikata ɓarna. Tsarin har wa yau na koyawa jama’a sanin muhimmancin ba da gudunmawa a matsayin su na ‘ya’yan al’umma, waɗanda suke da haƙƙin sa ido su ma kan abubuwan da ke faruwa a maƙwabtansu. 

Ko da ya ke a farko, an yi zargin su waɗannan ‘yan banga za su iya wuce gona da iri wajen ɗaukar doka a hannu, ko a haɗa baki da su da ɓata gari a aikata wata ɓarna, da kuma zargi wasu mambobinsu na iya zama tsoffin masu aikata laifuka ne da suka tuba, don haka za su iya sanya son zuciya a cikin aikinsu. 

A shekarar da ta gabata ta 2021 cikin watan Oktoba, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da amfani da sabon tsarin ‘Yan Sandan Al’umma da za a ɗauka aiki ƙarƙashin jagorancin Rundunar ‘Yan Sanda ta ƙasa tare da sanya hannu don cire kuɗi Naira Biliyan 13 da Miliyan 3 domin fara gudanar da wannan aiki, wanda bai samu bayyana ‘yan Nijeriya su tabbatar da abin da ake faɗa ba sai a cikin ‘yan makwannin nan, inda aka fitar da sabbin jami’an ‘yan sanda, kimanin dubu 20, domin a ƙara kan adadin jami’an ‘yan sandan da ake su a ƙasar nan, waɗanda aka daɗe ana kukan sun yi ƙaranci. 

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake kara kiraye kirayen ‘yan sanda su riƙa canja salon yadda suke mu’amala da mutane, don su bai wa jama’a damar sakin jikinsu su da jami’an tsaro har su iya shaida musu abin da suke nema na daga bayanan sirri. 

A sakamakon yadda ayyukan ‘yan ta’addan Boko Haram suka tsananta musamman a yankin Arewa maso Gabas a shekarun baya, gamayyar matasan Borno sun yunƙura don kare kansu da ba da gudunmawa wajen samar da tsaro a yankunansu, ta hanyar ɗaukar gorori da adduna domin farautar ‘yan Boko Haram, wannan yunƙuri shi ya haifar da abin da a yanzu ake kira da Sibiliyan JTF, wato gamayyar ƙungiyoyin matasa, ‘yan banga da maharba, don a tallafawa jami’an tsaro da ke yaƙi da ‘yan ta’adda. 

Wannan tsari ya samu goyon bayan matasa daga sassan ƙasar nan daban-daban, musamman a jihohin da ake fuskantar ƙalubalen tsaro irin su Kaduna, Katsina, Zamfara, Adamawa, Filato da Naija, saboda su ma su taimakawa jami’an tsaro a yankunansu. Ko da ya ke lokaci zuwa lokaci an sha samun rashin jituwa tsakanin waɗannan matasa da jami’an tsaro, ko jama’ar gari, inda har gwamnatocin wasu jihohin suka kafa dokokin haramta ayyukan ‘yan sa kai saboda yadda ake samun rahotannin ƙorafe-ƙorafe na ɗaukar doka a hannu ko haɗa ɓata gari. 

A ‘yan shekarun baya wasu rahotanni sun bayyana cewa sakamakon ƙalubalen tsaro da Jihar Zamfara ke fuskanta gwamnatin jihar ta ɗauki ‘yan ƙato da gora 500 a kowacce masarauta cikin masarautu 17 na jihar, wanda yawansu ya kai 8, 500 kuma tana biyansu Naira dubu 15 a kowanne wata duk domin inganta tsaro da kwanciyar hankali a jihar.

Wannan yunƙuri na gwamnatin jihar ya taimaka ainun sakamakon yawaitar yadda ake garkuwa da mutane a wasu wurare kan hanyar Zamfara zuwa Sakkwato, ‘yan kato da gora wato Civilian JTF da gwamnatin Jihar Zamfara ta ɗauka na ba da tsaro iya gwargwado, duk kuwa da ƙalubalen rashin makaman da za su iya tinkarar ‘yan bindiga, da kuma rashin gogewa.

Yana da kyau gwamnati ta samar da kyakkyawan tsari na horar da waɗannan matasa ‘yansa kai, tsakanin ‘yan banga da maharba, don ƙara sanin dokokin aiki da amfani da makamai yadda ya kamata, a kuma samar musu da alawus-alawus na ƙarfafa gwiwa ba wai a bar su haka kara zube ba, yadda zuciyarsu za ta kai su ga ba da kai bori ya hau a wajen ‘yan ta’adda. 

Jama’a su ma yana da kyau su fahimci cewa aikin tsaro na kowa da kowa ne ba sai ɗan banga ko ɗan ƙato da gora ba. Mu yarda cewa, ‘yan sanda ko sojoji da sauran jami’an tsaro ba za su iya yi maganin tsaro ba, sai mu da kan mu mun taimaka musu da bayanai da shawarwari kan yadda za a shawo kan matsalolin tsaro da suka dabaibaye al’ummarmu.

Mu sanya a ran mu cewa, kowannen mu ɗan sanda, a cikin gidajen mu, makwaftan mu, unguwanni mu, duk wani motsi da muka ji ko gani wanda ba mu yarda da shi ba to, lallai mu hanzarta kai rahoto ga wani ofishin jami’an tsaro mafi kusa.

Daga AHMAD MUSA, 07041094323.

By ukarofi