Mu guji siyasantar da sha’anin tsaro

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Rahotanni daga kafafen watsa labarai daban-daban sun rawaito Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zullum da Shaihun Borno, Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi, suna bayyana irin halin zullumin da Jihar Borno ta sake samun kanta a ciki na mamayar mayaƙan Boko Haram da dawowar ayyukan ta’addanci a wasu sassan jihar. Wannan ba rahoto ne mai daɗi ba.

A yayin da muke murna da samun nasarar da ake yi akan mayaƙan Boko Haram da cigaban da aka samu na zaman lafiya, a yankin Arewa Maso Gabas da wasu sassan ƙasar nan, fitowar wannan rahoto abu ne mai ɗaga hankali matuƙa.

Ko mako guda ba a kai ba, da Babban Mai Bai Wa Shugaban ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribaɗu, ya bayyana wa duniya cewa dakarun tsaron Nijeriya suna samun nasarori masu yawa a yaƙin da ake yi da ’yan ta’adda a sassan ƙasar nan. Tare da bayyana ƙwarin gwiwar sa kan nan ba da daɗewa ba za a cimma galaba kan duk wasu masu tayar da ƙayar baya a ƙasar nan. Amma babu shakka bayyanar wannan rahoto yana ƙara nuni da cewa akwai sauran rina a kaba.

A jawabin da Gwamna Zullum ya yi wa manema labarai bayan zaman Kwamitin Tsaro na Jihar Borno, ya yi zargin hankalin jami’an tsaro ya tashi daga yankin zuwa wani wajen daban, wanda hakan ya bai wa ’yan ta’adda damar sake dawowa da ƙarfinsu, sanin cewa babu dakarun soji masu yawa da za su iya tunkarar su. Ya roƙi Gwamnatin Tarayya ta dawo da hankalinta Jihar Borno, domin fuskantar waɗannan ’yan ta’adda yadda yakamata, gudun sake komawa gidan jiya.

Duk da nasarorin da jami’an tsaro ke samu akan ’yan bindiga a jihohin Zamfara, Sakkwato, Katsina da Kaduna, ’yan ta’adda na cigaba da haifar da ɓarna a, wasu yankunan. Kodayake, an samu sauƙin fargabar yawaitar satar mutane a kan manyan hanyoyin ƙasar nan, da kai wa ƙauyuka hare-hare cikin ayarin ’yan ta’adda. Amma ta bayan fage ana cigaba da halaka rayukan bayin Allah da jefa rayuwar ’yan Nijeriya cikin ƙunci da fargaba. Kamar abubuwan da suke faruwa na baya-bayan nan a Jihar Katsina da Jihar Filato.

Ba da jimawa ba, an samu rahotanni da ke bayyana cewa, wasu mahara sun kai hari kan wasu ƙauyuka a ƙaramar Hukumar ɓakkos ta Jihar Filato, inda aka samu salwantar rayuka da dama. Sannan a yayin da al’ummar Jihar Katsina ke murna da samun tsagaitawar hare-hare da kashe-kashe a cikin jihar, sai ga wani mummunan rahoto cikin wannan mako mai ƙarewa da ke bayyana cewa an kai wani hari a ƙauyen Maikuma da ke ƙaramar Hukumar ɗandume wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane huɗu tare da sace aƙalla 45 daga cikin mazauna yankin.

Shaidu sun bayyana cewa ’yan bindigar, waɗanda yawansu ya haura 100, sun mamaye ƙauyen ne ɗauke da muggan makamai, suna shiga gida-gida daga layi zuwa layi tsawon awanni kafin su tsere da waɗanda suka sace zuwa dajin da ke kusa da yankin.

Duk dai a cikin wannan lokaci da ake jimamin sake taɓarɓarewar sha’anin tsaro a yankin Arewa Maso Gabashin ƙasar nan, sai kuma ga wani rahoto daga yankin Kudu Maso Yamma inda ’yan ƙungiyar kare muradun ’yan ƙabilar Igbo, wato Ehanaeze Ndigbo, ta bakin Mataimakin Shugaban ƙungiyar na ƙasa Mazi Okechukwu Isiguzoro, ke kokawa da yawaitar kisan gilla a yankin jihohin ’yan ƙabilar Igbo, musammman a watanni huɗu na farkon wannan shekara. ƙungiyar ta yi zargin an kashe sama da mutane 300, sakamakon cigaba da taɓarɓarewar tsaro a yankin. Kar ku manta da kisan gillar Uromi da har yanzu ba a san ina aka kwana ba.

Lallai akwai abin ɗaga hankali da damuwa a ƙasar nan game da sha’anin tsaro, ba kamar yadda gwamnati ke so mu yi tunanin nasarorin da ake samu sun fi ƙalubalen da ake fuskanta ba. Ga duk me nazarin abubuwan da ke faruwa a ƙasar nan ya san akwai matsala sosai da ke barazana ga sha’anin tsaro a rayuwar ’yan Nijeriya, wanda ke buƙatar gwamnati da jami’an tsaro su ƙara ninka ƙoƙarin da suke yi.

Babu wanda zai yi musun cewa, ana samun nasara akan ’yan ta’adda, akwai cigaba sosai da ake samu saɓanin a watannin baya. Amma duk da haka ba zai hana a bai wa gwamnati shawara ba, kodayake babu abin da ba ta sani ba.

Mun ji yadda Tsohon Shugaban Shirin Hidimar ƙasa na NYSC, Manjo Janar Maharazu Tsiga ya faɗa bayan da ya samu ’yanci daga hannun masu garkuwa da mutane, ya bayyana cewa, a tsawon kwanaki 56 da ya shafe ana tsare da shi, ya lura babu abin da ’yan ta’addan ke tsoro irin shawagin jirgin yaƙi na soji. Wannan ya nunar mana da muhimmancin zafafa shawagi da kai hari kan maɓoyar ’yan ta’adda, da jiragen na zamani, don hana musu sakat ballantana su samu sukunin kitsa wasu hare-haren.

A daidai wannan gaɓar kuma ina so in yaba wa Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang bisa jajircewarsa akan sha’anin tsaro a jiharsa. Kamar yadda rahotanni ke cewa, gwamnatin jihar na shirin sayen jirgi marar matuƙi da zai riƙa shawagi yana binciken kaiwa da komowa kan sha’anin tsaro a jihar. Da fatan gwamnatin tarayya za ta mara wa gwamnonin ƙasar nan baya, su mallaki waɗannan jirage da kayan yaƙi na zamani da za su tallafawa jami’an tsaro da su.

Lallai akwai buƙatar amfani da sabbin makamai da aka ƙera da sabuwar fasahar zamani, don kai samame da saurin kai ɗaukin gaggawa, da tattara muhimman bayanai, da za su taimaka a samu galaba kan marasa zaman lafiya a ƙasar nan.

Muna fatan Gwamnatin Tarayya ba za ta maimaita kuskuren da tsohuwar gwamnatin Goodluck Jonathan ta yi ba, inda ta siyasantar da batun Boko Haram, tana kallonsa a matsayin wani makirci ne na ’yan Arewa don hana mulkinsa zaman lafiya. Wannan sakaci shi ya bayar da damar da ƙungiyar ta samu na yin ƙarfi da mamaye wurare da dama, da haifar da asarar ɗimbin rayuka da dukiyar da ba a san adadinta ba. Wannan tunani ya fara shigowa cikin wannan gwamnati mai ci, inda wasu da suke ganin magoya bayan shugaban ƙasa ne, suna faɗar irin waɗancan maganganu da a baya aka zargi ’yan Arewa da su.

Siyasantar da sha’anin tsaro ko alaƙanta shi da wani shiri na kawar da wata al’umma saboda dalilai na addini, babban kuskure ne da shugabanninmu ke yi. Tunanin su kawai shi ne siyasar su da neman goyon bayan jama’ar su, ba sauke nauyin da kundin tsarin mulkin ƙasa ya ɗora musu ba. Kuskure ne a samu wani Gwamna da zai riƙa maganganu na tunzura mutanensa akan wani addini ko ƙabila, yana mai ɗora alhakin gazawar tsaro a kan wasu mutane, don ba addininsu ko ƙabilarsu ɗaya ba.

Maganin matsalar tsaron da ake fuskanta shi ne kowa ya sa hannu a taimakawa gwamnati da jami’an tsaro, don shawo kan waɗannan matsaloli, a maimakon nuna yatsa ga wani ɓangare ko wata ƙabila. Haƙƙin kowa ne ya ba da gudunmawa a kowanne mataki, da dukkan damar da muke ita.

Allah Ya ba mu zaman lafiya da tsaro mai ɗorewa a jihohinmu da ƙasar mu bakiɗaya.

By ukarofi