Gwamnatin Katsina ta dakatar da hukumar ƙwallon ƙafa ta Katsina United

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Wannan mataki da gwamnatin Katsina ta ɗauka ya biyo bayan shan kaye da kungiyar ta sha a hannun ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta lkorodu City da ci shida ba ko ɗaya a gasar firimiya ta ƙasa.

Mambobi kungiyar da aka dakatar sun haɗa da Ghaddafi Muahammar Ruduwan da Abbas Tukur sai Abdullahi Umar leda.

Sauran sun haɗa da Yasir Yahaya da Abubakar Adidas tare da umurtan su da su miƙa kayayyakin ƙungiyar da ke hannu su zuwa ga babban sakataren a ma’aikatar matasa da wasanni Alhaji Rabiu Muhammad Rabiu.

Kwamishinan harkokin matasa da wasanni Aliyu lawal Zakari wanda ya sanar da dakatarwan ya sanar da naɗa Sake Yusuf da Aminu Lemo a matsayin waɗanda zasu jagoranci hukumar ƙwallon ƙafa 4 na wuccin gadi.

Wannan dakatarwan bai shafi mai koyar da ƙungiyar ba.

By ukarofi