Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara, ya gabatar da wani jawabi mai jan hankali inda ya jaddada cewa talauci ya fi yin barazana ga dimukraɗiyya fiye da rarraunan tsari a ƙasa.
Taron, wanda aka gudanar a otel ɗin Marriott da ke Ikeja, Legas, wanda ƙungiyar Coɓenant Nation ta shirya, ya mayar da hankali kan taken “Dimokraɗiyya da Tattalin Arzikin”.
A jawabinsa na buɗe taron, Dogara ya nuna jin daɗinsa ga waɗanda suka shirya taron, ya kuma yaba da taken da suka zaɓa, inda ya bayyana muhimmancinsa a ranar tunawa da dawowar Nijeriya kan turbar dimokuraɗiyya bayan shafe shekaru na mulkin soja.
Ya kuma jaddada gazawar dimokaraɗiyyar da ta shafe sama da shekaru ashirin ba tare da katsewa ba wajen tabbatar da ‘yancin tattalin arziki da zamantakewa ga ‘yan Nieriya, inda ya yi nuni da rashin tsaro, ingantattun kayayyakin more rayuwa, samar da ayyukan yi, da kuma abubuwan more rayuwa.
Dogara ya zurfafa cikin ma’anar dimokuraɗiyya, inda ya yi nuni da jaruman tarihin dimokuraɗiyya kamar su Magna Carta da fitattu irin sy Abraham Lincoln da Winston Churchill.
Ya bayyana tsarin Nijeriya a matsayin ƙasa mai bin tsarin mulkin dimokuraɗiyya da jaddada muhimmancin ƙa’idojin dimokuraɗiyya wajen tabbatar da adalci a zamantakewa.
