Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Sardaunan Funtua Alhaji Aƙilu Hassan Muhammad ya ce tallafawa matasa ne kawai zai kawo ƙarshen ta’addanci da sauran miyagun ɗabi’u a Katsina.
Alhaji Aƙilu wanda shine shugaban kamfanin sarrafa ƙarafa na NAK yayi wannan magana a garin Funtua a yayin da yake ganawa da manema labarai.
Ya bayyana cewa ganin yadda a ke samun yawaitar matasa a jihar,ya zama wajibi gwamnati da ƙungiyoyi masu zaman kansu da su ɓullo da hanyoyin tallafawa matasa domin a sami raguwar aikata ta’addanci da sauran miyagun ɗabi’u da ke addabar musamman kudancin jihar.
Aƙilu wanda ya aiwatar da shirye shirye da dama na tallafawa matasa a yankin,ya sanar da cewa yana nan yana lokacin samo rancen kuɗi Naira miliyan 20 damin rabawa matasan da ke da niyyar yin sana’a a yankin Funtua.
Ya ce har ya kafa kwamitin mutum biyar ƙarƙashin Sarkin Matasan Funtua domin samun nasarar shirin.
Ya kuma nuna takaicin sa yadda matsalar tsaro ke ƙaruwa a yankin,sai yayi kira da masu ruwa da tsaki da sauran al’umma da su tashi tsaye wajen yin mai yiwuwa na kawo ƙarshen ta’addanci a yankin da jihar Katsina baƙi daya.
