Hukumar tace finafinai ta Kano ta dakatar da muƙabalar mawaƙan addini

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Hukumar tace fina-finai da ɗab’i ta Jihar Kano ta haramta shirya duk wata muhawara a tsakanin mawaƙan addini, tare da gayyatar Usman Maidubun Isa, Shehi Mai Tajul’izzi da sauran wanda suka jagoranci muhawarar tasu dasu bayyana a gabanta a ƙasa da awa 24.

A wani yunƙuri na tabbatar da zaman lafiya, daidaito da bin doka tsakanin mawaƙa ɓangaren nishadi da na addini, shugaban hukumar tace fina-finai da ɗab’i ta Jihar Kano, Alh. Abba El-Mustapha, ya sanar da haramta duk wani nau’in muhawara daga mawaƙan addini a Jihar Kano, ba tare da izinin hukumar ba.

Ta cikin wata sanarwar da mai magana da yawun hukumar Abdullahi Sani Sulaiman ya raba wa manema labarai a yau, ya ce wannan mataki ya biyo bayan wata muhawara da aka gudanar ba tare da izinin hukumar ba tsakanin Usman Maidubun Isa da Shehi Mai Tajul’izzi, wacce hukumar ta bayyana ta a matsayin karya dokokin aikinta.

A yayin da yake ƙaddamar da kwamitin bincike wanda Mal. Isha Abdullahi, Daraktan Ayyuka na Musamman na hukumar zai jagoranta, Abba El-Mustapha ya bayar da wa’adin sa’o’i 24 ga mawakan da wanda suka jagoranci muhawarar tasu da su bayyana a gaban kwamitin domin amsa tambayoyi.

Kazalika, hukumar ta ce shirya irin waɗannan muhawarori ba tare da sahalewar ta ba, ya keta dokar da ta kafa hukumar, kuma ka iya jawo hukunci mai tsanani ga wanda suka aikata hakan.

Abba El-Mustapha ya jaddada ƙudurin hukumarsa na ci gaba da kula da ayyukan mawaƙa da masu nishaɗantarwa a faɗin jihar bisa doka da ƙa’ida. Ya kuma buƙaci al’umma da su zauna lafiya, tare da bayar da haɗin kai da kawo bayanai masu amfani domin tabbatar da zaman lafiya, fahimtar juna da ci gaban al’adu a jihar Kano.

A jiya Litinin ne dai Mawaƙan biyu suka yi muƙabala kan wani Hadisin Sahabin Ma’aiki S.A.W. Jabir, wanda hakan ya jawo cece kuce a Kafafen sada zumunta da al’ummar jihar Kano.

By ukarofi