Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan Jihar Neja, Umaru Bago ya amince da tireloli biyu na buhunan shinkafa mai nauyin kilogiram 50 ga ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa, NLC, a matsayin tallafin rage raɗaɗin cire tallafn man fetur.
Mista Bago ya sanar da amincewar ne a lokacin liyafar murnar sabon ginin ofishin mataimakin gwamna, Yakubu Garba da aka gina a Minna.
Ya bayyana cewa Naira miliyan 110 da aka amince wa ƙungiyar ta NLC tun da fari, an ba su ne don samar da kayan aiki don sanya ido kan yadda ake raba kayan agajin a mazaɓu 274 na jihar.
“Ma’aikata, mun ba ku aikin zagayawa don kula da yadda ake rabon kayan tallafi, amma ga ƙungiyar ƙwadago, ba mu ba ku kayan tallafi ba.
“Mun ba ku kayan aiki ne kawai don ku zagaya don kula da rarrabawa, yanzu a matsayin gwamnati, za mu ba ku tirelar shinkafa mai nauyin kilo 50 guda biyu don rarrabawa,” inji shi.