Gwamnatin Sin ta sanar da bayar da tallafin dala miliyan 500 ga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), wanda zai kasance cikin shekaru biyar masu zuwa. Wannan kuɗin na zuwa ne a lokacin da Amurka ta rage goyon bayanta ga WHO, lamarin da ya sanya hukumar ta fuskanci matsaloli wajen gudanar da ayyukanta.
Liu Guozhong, mataimakin firayim ministan Sin, ya bayyana cewa, wannan tallafi yana nufin ƙarfafa haɗun gwiwar ƙasa da ƙasa a fannin lafiya, tare da tabbatar da cewa, duniya ta samu damar daƙile cututtuka da sauran barazanar lafiya a gaba. Wannan matakin Sin na ƙara nuna cewa, tana son ɗaukar jagoranci a fannin kiwon lafiya a duniya, inda ta fi mayar da hankali kan samar da magunguna, rigakafi da inganta tsarin kiwon lafiya a ƙasashe masu tasowa.
Masana harkokin siyasa sun nuna cewa, wannan ne wani ɓangare na dabarar Sin ta ƙarfafa matsayin ta a fagen kasa da kasa, musamman ma bayan ficewar Amurka daga WHO a wani lokaci da aka yi zargin rashin goyon baya da jagoranci mai ƙarfi daga Amurka. Wannan yana nufin Sin na amfani da damar don ta ƙara tasiri a matakin duniya, musamman a lokacin da ake fama da cututtuka kamar Korora da sauran matsalolin lafiya.
