
Daga BELLO A. BABAJI
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya taimaka wajen ƙawata makarantar ƴan baiwa ta School for the Gifted dake Gwagwalada, kamar yadda Shugaban makarantar Bello Adamu Audu ya bayyana.
Ya bayyana gyara makarantar a matsayin farfaɗo da martabarta a lokacin da take neman rugujewa.
Ya ce kafin Ministan ya kawo ɗauki, makarantar tana halin neman agaji, inda bangunanta suka ƙoƙe da kuma tsufa da wasu ababen amfani suka yi waɗanda suke ƙoƙarin hana cigaba da karantarwa.
Tallafin da Minista Wike ya bayar, ya taimaka wajen sanya sababbin fankoki da fente bangunan makarantar da kuma yin wasu gyare-gyare da suka samar da yanayi mai kyau na cigaba da karatu ga ɗalibai da malamai.
Ɗalibai da ma’aikatan makarantar sun bayyana godiyarsu ga Ministan ganin yadda aka dawo da martabar makarantar.
Shugabar ɗaliban makarantar mai suna, Abdulraheem Taofeeqiyyah ta jinjina wa hoɓɓasa da ministan ya yi, ta na mai jaddada tasirin hakan ga karatun ɗalibai.
