Tarihin Nana Faɗima ‘yar Manzon (3)

Daga MOHAMMED BALA GARBA, MAIDUGURI

Haƙƙoƙin Ahlul Baiti a Kan Al’umar Musulmai

Iyalan gidan Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wasallam) suna da waɗansu haƙƙoƙi guda Uku (3) waɗanda suka zama wajibi a kan kowane Musulmi. Ga su kamar haka:

Ƙauna da Girmamawa:

Iyalan gidan Manzo suna da wananan matsayi a cikin al’umma, dake wajabta a kaunace su da girmama su fiye da kowa. Abubuwan da muka ambata a baya ma sun isa hujja a kan wannan. Ba sai mun nemi kafa wata sabuwar hujja ba.

Yi musu salati tare da mai gidansu:

Yi wa Ahlul Baiti Salati tare da Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wasallam) na daga cikin haƙƙoƙinsu a kan Musulmi mai bin tafarkin Sunnah. Don Allah (SWT) ya ce: “Lalle, Allah da Mala’ikunsa suna Salati ga Annabi. Ya ku waɗanda suka yi imani ku yi Salati a gare shi, kuma ku yi Sallama domin amintarwa a gare shi.” Kuma Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wasallam) da ya bayyana wa Sahabbai yadda wannan Salati zai kasance, ya gaya musu su shigar da iyalansa. Mun kawo wannan hadisin a can baya.

Biyayya:

Biyayya da koyi da su, shi ma wajibi ne, a kan duk wanda ke koyi da Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wasallam).

Wace Ce Nana Faɗima?

Ita ce Fadimatul Zahra’u ‘yar shugan halitta Annabi Muhammadu (Baban Alkasim), ɗan Abdullahi ɗan Abdulmuddalib ɗan Hashim ɗan Abdumanaf ɗan kusaiyi ɗan Kilab ɗan Murrah ɗan Ka’ab ɗan Lu’a’iyi ɗan Galib ɗan Fihri ɗan Malik ɗan Nadri ɗan Kinanah ɗan Khuzaimah ɗan Mudrikah ɗan Iliyas ɗan Mudar ɗan Nazar ɗan Ma’add ɗan Adnan. Wannan ita ce dangartakarta wacce babu sabani akai, kamar yadda kuma ba a yi sabani ba wajen cewa “Adnan” ɗaya ne daga cikin zurriyar Annabi Isma’ilu. (Wato kenan dangantakan Annabi (Sallalahu Alaihi Wasallam) ta haɗu da ta Annabi Isma’ilu ɗan Annabi Ibrahimu).

Haihuwarta:

An haifi Nana Fadimatul Zahra’u (Allah ya kara mata yarda) ne a ranar Juma’a, Ashirin ga watan jimada sani, shekaru biyu bayan aiko Annabi Muhammadu (Sallalahu Alaihi Wasallam). Bayan haihuwar Manzo Allah (Sallalahu Alaihi Wasallam) ya amshi ‘yarsa da farin ciki da amincewa, ya kuma sa mata suna Faɗima.

An haife ta kuma ta tashi a gidan Annabci, ta tarbiyyantu a inuwar wahayi, da kyawawan ɗabi’u daga uwar muminai Nana Khadija (Allah ya kara mata yarda). Nana Faɗima ta kasance mai dauke da ruhin Manzo Allah (Sallalahu Alaihi Wasallam) da ɗabi’unsa, don haka ta zama mai gado da kuma tsananin kama dashi.

Ban ga wanda ya fi kama da Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wasallam) a rashin magana da kyauta fiye da Nana Faɗima ‘yar Manzon Allah ba, a tsayuwarta da zamanta. Ta kasance idan ta shiga wajen Annabi (Sallalahu Alaihi Wasallam) ya kan mike ya tarbe ta, ya zaunar da ita a wurin zamansa.

Haka nan idan Annabi ya shiga gare ta, ta kan mike daga wajen zamanta ta tarbe shi, ta zaunar da shi a wajen zamanta. “Allah Ya so Fadima ta fara yarintarta a wani yanayi mafi tsananin wahala da kuntatawa daga matakan da’awar Musulunci, kuma wanda mahaifanta suka fi shan wahala da cutuwa a cikinsa.

Ga dai Ƙuraishawa nan na tilasta takunkumi tattalin arziki a kan Manzon Allah da danginsa daga Banu Hashim da mayar da su saniyar- ware.

A wannan lokacin ne aka tsare Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wasallam) a Shi’abu Abu Dalib tare da matarsa Nana Khadija da ‘yarsa Nana Faɗima da sauran Musulmi. Shekarun takunkumi sun wuce tare da matsanancin hali, har zuwa lokacin da Manzo (Sallalahu Alaihi Wasallam) ya fita daga cikinsa tare da waɗanda ke tare da shi alhali Allah ya rubuta masa nasara da galaba. Khadija kuwa ta fita daga cikin shi alhali shekarun sun yi mata nauyi, gajiyar takunkumi da matsalolinsa sun raunana ta.

Wannan ya sa ajalinta ya gabato. Allah ya zabar mata maƙwabtakarsa, inda ta rasu a wannan shekara, bayan ‘yan watanni kuma sai Abu Dalib baffan Annabi (Sallalahu Alaihi Wasallam), mai ba da kariya da taimakon Musulunci, wanda Manzo (Sallalahu Alaihi Wasallam) ya bayyana yadda ya yi rashinsa da fadarsa cewa:

“Kuraishawa ba su fara matsamin ba har sai da Abu Dalib ya yi wafati har sau biyu’’” (ya rasu).

Haƙiƙa Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wasallam) ya yi bakin ciki kuma ya ji kaɗaici saboda rabuwa da Nana Khadija. Domin ya yi rashin Khadija matarsa, masoyiyarsa kuma mai taimakonsa. Kamar yadda ya yi rashin baffansa mai kariya gare shi, don haka ya kira wannan shekara da sunan shekarar bakin-ciki.

Nana Faɗima, ƙaramar ‘yar Manzo Allah (Sallalahu Alaihi Wasallam) (a wannan lokaci) haka ta rayu cikin wani ɓangare na wannan bakin ciki, ita ma ta yi makoki, don kuwa ita ma bala’in wannan shekarar ya taba ta, yayin da ta rasa uwa mai tausayi, alhali kafin nan ta koshi da ƙaunarta da lurarta, don haka (yanzu) ta lullubu da baƙin-ciki da maraici. Sanannen abu ne cewa dole ne wannan rasuwa ta girgiza Nana Faɗima don kuwa ta rasa mahaifiyarta, ta rabu da cibiyar ƙaunarta, don haka sai dacin rabuwa ya cika zuciyarta ya kuma girgiza ta.

Babanta Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wasallam) ya dandana baƙin-ciki Nana Faɗima, yayin da ya ga ƙaramar ‘yarsa na zubar da hawayen rabuwa da mahaifiyarta, sai zuciyarsa mai tausayi ta yi kuna, jiyayyar nan tasa ta uba mai kauna ta gaskiya ta tabu, don haka sai ya kusanci Nana Faɗima don ya musanya mata abin da ta yi rashi na ƙauna da kusanci da ƙaunarsa da taushin zuciyarsa.

Haƙiƙa Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wasallam) ya so Nana Faɗima kuma ita ma ta so shi, ya tausaya mata kuma ita ma ta tausaya masa. Babu wanda ya fi Nana Faɗima kusa da shi kuma ba wanda yake so kamar ta. Ya sha jaddada wannan alaƙa a cikin hadisansa yana bayyana matsayinta a cikin al’ummarsa. Ga kaɗan daga cikin abubuwan da ya faɗi dangane da ita:

“Faɗima wani yanki ne daga gare ni, wanda ya fusata ta ya fusata ni.” Duba Bukhari hadisi na (3714).

Da kuma cewa: “Lallai Faɗima wani yanki ne daga gare ni, (duk) abin da ke cutar da ita yana cutar da ni “. Bukhari hadisi na (3714).

A wani wajen kuma cewa ya yi: “Ya Faɗima, ashe ba za ki yarda da kasancewa shugabar matan duniya ba, kuma shugabar wannan al’umma da shugabar matan Muminai. Bukhari hadisi na (3715 dana 3716).

“Fadima na girma ƙaunar babanta na girma tare da ita, tausayinsa na ƙaruwa, kuma ita ma tana musanya masa wannan ƙauna, tana cika zuciyarsa da lura, don haka ya kira ta da Ummu Abiha (wato uwa a wajen babanta)

“Ta kasance tana ji da shi da tausaya masa irin tausayin uwa ga ‘ya’yanta, tana kuma lura da shi kamar yadda uwaye mata ke lura da ‘ya’yansu ƙanana, wanda hakan ya zamanto abin koyi ne na tsarkakkar alaƙar uba (da ‘ya’yansa) wajen gina ‘ya’ya da fuskantar da ɗabi’u da rayuwarsu, da cika zukatansu da ƙauna da tausayi.

Haƙiƙa wannan alaka ta zama babbar abar misali a fagen renon ‘ya mace a Musulunci da lura da ita, girmamata da ɗaukaka matsayinta. Domin Karin bayani sai a duba: Hakim, Mustadrak al-Sahihain, juzu’i na 4, shafi na 272 da Bukhari Adabul-Mufrad, shafi na 136 da Abu Dauda, Sunan, juzu’i na 2, shafi na 354 da Sahih Tirmizi, juzu’i na 2, shafi na 319 da Hakim, Mustadrak al-Sahihain, juzu’i na 2, shafi na 626.

Arbili ya fitar da shi da wasu lafuzzan a cikin Kashful-gummah, juzu’i na 1, shafi na 16. da Bukhari, al-Sahiha, juzu’i na 2, shafi na 185 da Ahmad ɗan Hambali, Musnad, juzu’i na 4, shafi na 332 da Hakim, Mustadrak al-Sahihain¸juzu’I na 3, shafi na 154 da Ahmad ɗan Hambali, Musnad, juzu’i na 4, shafi na 5; da Nasa’i, Khasa’isu Amirul-Mu’uminina Ali ɗan Abu Dalib, shafi na 25 (a ciki ya zo da ƙarin cewa: wanda kuwa ya cutar da Manzon Allah aikinsa ya baci) da Idan al-Athir, Usudul-Gaba, juzu’I na 5, shafi na 520, da Idan Abd al-Bar, al-Isti’ab, juzu’i na 2, shafi na 752

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *