Taron addu’ar bakwai: ‘Yan Fim sun bayyana kyawawan halayen Furodusa Umma Ali

Daga MUKHTAR YAKUBU, a Kano

Bayan kwanaki bakwai da rasuwar Furodusa Umma Ali, gamayyar ƙungiyoyi da suke gudanar da harkokin sana’ar su a cikin masana’antar finafinai ta Kannywood bisa jagorancin Ƙungiyar Ƙwararru ta Masu Shirya Fim ta Ƙasa (MOPPAN) sun shirya taron addu’ar cika kwanaki bakwai da rasuwar Uwa kuma ɗaya daga cikin dattawan masana’antar Furodusa Umma Ali wadda Allah ya yi wa rasuwa a ranar Lahadi, 1//8/2021.

Taron wanda aka gudanar a Majalisar Matasa ta Tarauni da ke unguwar Gyaɗi-gyaɗi za a iya cewa ya bambanta da sauran taron da ‘yan masana’antar suka saba shiryawa musamman a wannan lokacin, ya samu halartar masu ruwa da tsaki a cikin harkar da kuma kusan dukkan ɓangarorin da su ke gudanar da sana’a a masana’antar.

Bayan gudanar da dddu’o’i da aka yi na tsawon lokaci ga marigayiyar, da sauran ‘yan fim da suka riga mu gidan gaskiya, kuma an yi addu’ar neman mafita dangane da neman mafita a wajen Allah bisa halin da masana’antar ta samu kanta, sannan kuma jama’a da dama cikin makusanta da kuma abokan sana’ar marigayiyar sun yi bayani a kan kyawawan ɗabi’u na Hajiya Umma Ali, da kuma irin gudummawar da ta bai wa harkar fim tsawon shekaru masu yawa.

Ado Ahmad Gidan Dabino MON wanda furodusa ne kuma jarumi da ya daɗe ana damawa da shi, ya bayyana rasuwar Furodusa Umma Ali da babban rashi, in da yake cewa; “Abin da zan ce dangane da rasuwarta, lallai an yi babban rashi sosai, domin a sani na da Hajiya Umma tsawon shekaru, na san mace ce mai hakuri, kuma ta na taimakon wannan masana’anta don haka samun kamar ta a wannan yanayin, abu ne mai wuya, domin ta kasance gidan ta kamar gidan ‘yan fim ne, kowa ya zo gidan sa ne, don haka wannan wani abu ne da ba kowa ne zai iya yi ba, don haka za mu daɗe muna tunanin wannan rashi da muka yi na Hajiya Umma Ali.”

Shi ma ɗaya daga cikin mutanen da suka ci gajiyar marigayiyar, wato MC Ibrahim Sharukan, ya bayyana cewar, “To a matsayina na ɗa a wajen ta wanda duk wani abu nawa a masana’antar fim ita ce babu abin da zan ce, domin ban da mahaifiyata ita kaɗai ce ta zamo uwa a gare ni. Kuma irin tallafin da ta bayar a wannan masana’antar zan iya cewa kowa ma zai zama uwa ce a gare shi.

“Sannan kuma irin taimakon da Hajiya ta ke yi a rayuwar ta ba a san iya adadin mutanen da ta raina ba, misali kamar irin mu da muka zamo fitattu ni Ibrahim Sharukan tare da Dauda Kahutu Rarara duk a gidan ta muka tashi, kuma duk ita ta raine mu, kuma gaskiya dukkan ‘yan fim wanda bai yi rayuwa a gidan ta ba, sai dai na wannan lokacin, kuma duk wani ɗan fim, ka ga dai mutanen da suka taru a wajen nan kowa yana yabon ta, don haka arziki ne, don ta mutu a gidan mijin, ‘Ya’yanta na yabon ta, dangin ta na yabon ta. Muna roƙon Allah ya jiƙan ta, Allah ya yi mata rahama, Allah ya sa halin ta nagari ya bi ta, don haka ina yi wa kowa fatan alheri.”

Shi ma shugaban ƙungiyar MOPPAN na ƙasa, Dakta Ahmad Sarari, ya bayyana rasuwar Hajiya Umma Ali da cewar, “kamar yadda masu bayani suka yi a wannan taro dangane da wannan baiwar Allah, to lokaci ba zai Isa ba na a bayyana kyawawan halaye na Hajiya Umma Ali don irin gudummawar da ta bai wa masana’antar abu ne da ya ke a bayyane, don mun taso mun same ta a cikin masana’antar, kuma duk buƙatun mu da mu ke aikawa ko mu je da niyyar neman taimakon ta ba mu ba a tava samun matsala ba, kuma duk lokacin da za mu yi taro to abincin mu a gidan ta ya ke, in wata ta zo baquwa a gidan ta ne masauki don haka babu abin da za mu ce sai dai Allah ya yi mata Rahama.”

Ita ma babbar aminiyar ta a cikin masana’antar Hajiya Balaraba Ramat Yakubu, ta bayyana Hajiya Umma a matsayin mai haƙurin zama da jama’a, domin a cewar ta tsawon zama da suka yi da ita babu wani abu da ya tava haɗa su, don haka ta bayyana marigayiyar a matsayin abin koyi.”

Taron addu’ar dai ya samu halartar ‘yan fim da suka haɗa da Shu’aibu Yawale, Kabiru Maikaba, Alhassan Kwalle, Adamu kwabon Masoyi, Bala Anas Babinlata Ahmad Alkanawy, da sauran su.