Mijin Bahaushe: Sulhu alkhairi ne

Daga AMINA YUSUF ALI

Barkanku da jimirin karatun Manhaja. A wannan mako mun zo mu ku da bayani a game da yadda za a gyara aure a gidan Malam Bahaushe. Saboda a zahirin gaskiya, rayuwar auren Bahaushe tana cike da rashin ha}uri da rashin fahimtar juna. A kullum idan aka samu kuskure daga namiji, sai iyaye su tursasa ‘ya’yansu mata su yi haƙuri su zauna da shi, su yi addu’a tare da fatan shiryiwa a gare shi. Ko da kuwa laifinsa na zina ne, ko dukan mace, ko ƙaurace mata, ko hana ta haƙƙoƙin da Allah ya ɗora masa nata. Shin su ma maza ana yi musu irin wannan nasihar?

Idan ya kama matarsa da laifi a ce masa ya je ya cigaba da haƙuri da yi mata fatan ta gyara? Gaskiya hakan yana da matuƙar wahala. Sai dai ma idan ya ba wa iyaye, ko dangi ko abokansa labarin rashin kyautatawar matarsa, sai a dinga bijiro masa da zancen ya rabu da ita. Ya sake ta kenan ko a ce masa ya ƙaro mata, hakan zai sa ita uwargidan ta gyara halayenta?

Dukka waɗannan abubuwa biyu wato saki da ƙaro auro da ake kawowa a matsayin maslaha ga namiji su ne kaɗai maslaha? Kada mu manta fa al’ummar Bahaushe da ma ta yi ƙaurin suna wajen auri-saki da yawan mace-macen aure. Anya ba za mu sauya tunani ba? Anya tunda dama ta ƙiya ba za mu koma hagu ba? Anya ba za mu dinga sulhu ba mu fahimci juna maimakon kullum ana saki ana ƙaro auren amma ba canji. Kuma ga shi shi wannan saɓani wajibi ne a cikin dukkan wata alaƙa. Tsakanin ‘yanuwa ma ana yi ko abokai. To me ya sai ɓarakar aure ce ita ma ba za a bi ta da allura da zare a ƙinke ta ba?

 Misali namiji ya kawo ƙorafin matarsa ga danginsa tana yin wasu abubuwan da bai kamata ba. Sai kawai su ba shi shawarar ko dai ya ƙaro auren ko kuma ya sake ta. Wanda hakan ba ita ce shawarar da ta kamata ba. Me ya sa ba za a zauna a gyara ba? Na ga maza da yawa da suka ƙaro aure ko suka rabu da matansu suka auri wasu.

Amma sai matsalolinsu suka ƙara ta’azzara. Kuma ya afka kogin da na sani. Ba mamaki fa har da rashin ba su shawara mai kyau daga magabata. Sannan wani abun idan ya gagara ai addu’a ake yi. Sai Allah ya shigo lamarinku ya yi gyara.

A addinace ma fa sulhu aka koyar da mu a aure. Musulunci ya samar da matakai na sulhun ma’aurata. Tun daga matakin sulhu a tsakaninsu har zuwa sulhu a tsakanin magabatansu. Sai idan abin ya ci tura ne, kuma rabuwar ta fi alfanu, sai a rabu ɗin. Ma’aurata ku matso ku ji. Gara ma namiji ya haƙura da wacce yake tare da ita in dai ba wani mugun hali ne da ita ba wanda ka san zai iya gurɓata maka zuri’a. Duk da dai mata da yawa suna da wasu mugayen hali da suke yi domin wahalar da mazaje.

Musamman ma idan sun ga su kaɗai ne ba su da kishiyoyi. Su sani idan ba su gyara hali ba, suka tunzura namiji zuwa bangon ƙarshe zai iya rabuwa da su. Idan kuma rabuwa ta afku, sai ka ga dukkan ɓangarorin an afka a kogin nadama. To me ya yi zafi da ido zai ci wuta? To kowa ya gyara mana.

Hanyoyin da za a bi a kiyaye hakan sun haɗa da, idan saɓani ya afku a gidan aure, kawai sai wanda ya san shi ne da laifi ya fito ya amsa laifin ya ba da haƙuri. Ba kuma wai ba da ha}uri kawai ba, a ba da haƙuri da zuciya guda. Ba wai ka ce na san laifina ne amma kaza-da-kaza. A’a ba da haƙuri kawai. Idan macen ce ma haka.

An san dai da matuƙar wahala hakan. Musamman ma a wajen maza. Suna ganin kamar zub da girma ne ko ja wa kai raini ne ya nuna ya amshi laifinsa. Amma zai samu kwanciyar hankali. Shi girman kai rawanin tsiya ne. Sam ba shi da riba sai asara. Ma’aurata ku sauke girman kai. Ko don kwanciyar hankalin yaran da suke tsakaninsu. Ita da ma mace a shar’ance ita ce a ƙasa.

Shi kuma namiji shi ma ya ajje girman nasa ya amsa laifinsa. Ya daina ganin zaman aure a matsayin alfarma ga mace. Sai auren ya mutu kuma, sai ya gane shayi ruwa ne. Wani ma sai bayan guri ya ƙure masa zai gane illar rabuwa da mace mai yara. Gabaɗaya hankalinsa da nata ba zai ƙara kwanciya ba. Ko da ta yi wani auren ko shi ya yi wani auren.  Kullum yana tunanin yadda ake riƙe masa yara. Ya ƙi haƙuri da uwarsu ga shi kuma dole ya yi haƙuri da wata, ba yadda zai yi. Ita ma idan ya saka, bai sn wacce zai jajibo ba. Wani mafarin aure-aurensa kenan. Ko da ba shi da ra’ayin tara mata.

Don haka, dole a ƙara haƙuri da abokiyar zama. Mace ce fa. Kuma shekarunsa mai yiwuwa sun ninka nata. Ga hankalinsa ba irin nata ba. Don haka dole ka yi uzuri mai tsaho. Sannan kuma dole ya koyi yafiya mai yawa. Idan ba haka ba, ya biye wa shawarwarin sakin ta ko ƙaro mata kishiya, kwaɓarsa za ta yi ruwa.

Kuma ba ƙarin auren aka ce babu kyau ba. Amma ka ƙaro aure don Allah (SWT), don raya sunnar Manzon Allah (SAW). Ba wai don kana son ka rama abinda matarka take maka ba. Ko kuma don kana so ka gyara halinta ba. Haka rabuwa idan ta zo, a rabu saboda ita ce maslaha. Ba wai don ka hukunta matarka a kan laifin da ta yi maka ba. Wannan babban kuskure ne.

Eh an san idan an yi rabuwar aure mace da iyayenta a lokacin da abun ya faru, sun fi tagayyara musamman ma idan da yara a tsakani. Amma fa shi ma namijin yana ɗanɗana tasa kuɗar duk da dai shi sai a gaba zai fuskanci shi ma abin ya shafe shi, matuƙa.


Sannan kuma ya kamata idan saɓani ya faru a tattauna matsalar a wuce wajen. Kada a ce za a yi gaba ko a ƙullaci juna. Ko kuma a ce wai sai an yi ramuwar gayya wacce Hausawa kan ce ta gi ta farau zafi. Irin dai yadda abokan gaba suke yi min kan kara, na yi maka na itace. Kuma su sani, gaba da riƙon juna ba ƙaramar illa yake kawowa ba a zaman aure. Gaba tana ƙara sawa a nesanta da juna. Kuma rashin fahimta ta ƙara tsananta a gidan auren. Har wani lokacin ma ya kawo rabuwa.

Idan an samu rashin jituwa a tsakanin ma’aurata, ya kamata bayan sun sakko, fushi ya ɗan ragu, to a zauna a tattauna matsalar. Barin matsaloli su taru a tsakaninsu shi ne a ma fi yawan lokuta yake rusa aure. Ba a tsaya an fuakanci juna ba. Kowa ya ƙullaci abokin zamansa .Kuma ƙullatar abokin rayuwa a zuciyarka shi yake sawa soyayya da kyautatawa gare su ita ma ta ragu. Idan abu ya wuce, kawai ya wuce. A yafe wa juna kuma a kiyaye gaba. Hakan shi ya kamata, ba wai rabuwa ba.

Sannan kuma kada namiji ya dinga ɗauka kullum shi ne a dai-dai. Ya kamata a ce idan matsala tana yawan faruwa da iyalinsa, ya zauna ya yi karatun ta-nutsu ya ga anya shi ma ba shi da wani hali da yake buƙatar ya gyara? Idan ya gano, sai ya gyara a zauna lafiya. Idan tunaninsa bai iya ba shi amsa ba, zai iya tamabayar matar ya ji ta bakinta. Cikin dabara suna raha, ya ji wai shin daga cikin halayensa wanne ne yake ci mata tuwa a ƙwarya? Za ta iya sakin jiki ta gaya masa. Shi kuma zai amfani da hikima wajen ganin ya gyara.

Bayan haka kuma ma’aurata su sani, aure fa ibada ne ba wai gidan ɓarje gumi ba. Ibada kuma ba ra’ayi ce ba. Bin umarnin Allah ne, tsantsa ba son rai ba. Haka kuma dole idan za a gina alaƙa mai ɗorewa, ana buƙatar sadaukarwa. Dole sai an haƙura da wani jin daɗin sannan a gina rayuwa mai kyau. Sannan a sama wa zuriyya makoma mai kyau.

Su ma mata a nasu ɓangaren, ya kamata su zama masu haƙuri da biyayya. Ki guji tunzura miji ta hanyar ramuwar gayya a kan dukkan abinda ya yi miki. Idan laifi ne ki zauna ku sasanta. Idan sasancin bai yiwu ba, ki zamo mai yawan yafiya da uzuri. Ki guji yi masa abinda zai tura shi ya sake ki. Ki dinga tunawa da makomar ‘ya’yanki.

Sannan ki tuna a cikin al’ummar da kike. Wacce take ganin laifin bazawara amma ba ta ganin laifin wanda ya yi sakin. Sannan kuma ki tuna sai kin fi tagayyara fiye da mijinki. To me ya yi zafi? Ki kama kanki, ki zauna lafiya da mijinki kamar yadda Allah ya shar’anta.