Anya ‘yan Arewa mun san waɗannan ni’imomin da Allah Ya yi wa yankinmu?

Daga BASHIR IBRAHIM NA’IYA

Kaɗan daga cikin ni’imomin da Allah Ya yi wa yankin Arewa su ne: yawan al’umma, mayalwaciyar ƙasar noma, dabbobin kiwo. Shin muna godiya ga Allah ta hanyar sarrafa wadannan ni’imomin da ya yi mana a yankinmu?

An ce yawan mutane shi ne kasuwa. Wannan dalilin ya sa nake ganin duk kamfanonin kayan abinci da sauran kayan amfanin yau da kullum na yankin Kudu, kasuwancinsu kacokam ya dogara ne ga yankin Arewa. Domin kuwa, mun fi su yawa sosai. Ƙaramin misali anan shi ne, ‘yan watannin baya kadan, ‘yan Areawa sun yi yajin aikin safarar kayan abinci zuwa Kudu. Wannan al’amari ba karamin girgiza Kudun ya yi ba.

A ɗan ƙaramin lokaci sun shiga cikin barazanar matsalar ƙarancin kayan abinci. Shin kun ji su ma sun dauki irin wannan matakin na hana kawo kayan masarufi da kayan abincin da kamfanoninsu suke sarrafawa zuwa Arewa? Ko da wasa ba su yi hakan ba. Ni da a zato na, na ɗauka su ma za su ɗauki wannan matakin.

Wani rahoto da ban tabbatar da shi ba, shi ne, na dai an ce su ma za hana kawo mana goro daga Kudu, in har gaske ne, wannan ya zama abin dariya. Abin da nake son fito mana da shi a nan shi ne, ko da wasa ba za su taɓa iya daukan irin matakin da muka ɗauka ba, su hana kawo mana kayan kamfanoninsu saboda mun hana kai musu kayan gona.

Domin kuwa, idan suka yi haka, to tamkar sun yi kirari ne, suka daɓa wa kansu wuka. To kun ga kenan, ni’imar da Allah ya yi mana ta yawan al’umma ta yi mana rana kenan. Kuma a Najeriya Arewa ita ce ƙasar da da a ce manyanmu sun yi amfani da wannan ni’imar ta yadda ya dace, da sam ba za mu dinga fuskantar cin kashin da yan kudu suke yi mana ba.

Cikin hikimar Ubangiji da yai mana, da ya ba mu yawan al’umma, cikin hikimarsa sai ya bamu kasar noma. Za ku gane haƙiƙa wannan ba ƙaramar ni’ima ba ce. Idan ku ka yi duba ga jihohin Kudu, mu ɗauki misalin jihar Legas. Idan kuka ɗauke Kano, Lagos ita ce jahar da ta fi kowacce jaha yawan al’umma a kasar nan. Amma Allah cikin ikonsa, bai ba su ƙasar noma ba. Kaso ma fi tsoka na faɗin jahar duk ruwa ne.

Akwai ma da yawa waɗanda suke rayuwa akan ruwa. Amma sai suka sarrafa ruwan ya zama babbar hanyar samar da ayyuka da samun hanyoyin kuɗaɗen shiga. Har ya zama sun fi kowacce jaha samun kuɗaɗen shiga. Duk da wannan arzikin ruwan da Allah ya ni’imanta jahar Lagos da shi, amma har yanzu ɗin nan, babbar damuwarsu ko matsalarsu ita ce kasar noma.

A ‘yan kwanakin baya kaɗan, Gwamnatin jahar Lagos, ina jin har ma da wasu jahohin yankin, sun yi taro akan yadda za su rage dogaro da kayan amfanin gonar da ake shigo musu da shi daga Arewa. A taron, sun kafa wani babban asusu don yin aikin rage dogaro da shigo musu da kayan abincin. Kun san wacce shawara suka yanke? Sun yanke shawarar zama da wasu daga Gwamnonin Arewa, akan za su zo jahohinsu su fara noma kayan abincin da za su dinga kai wa jahohinsu. Me hakan yake nufi? Hakan na nufin Arewar dai, wato Arewa ta zama dole a tafi da ita ko an ƙi ko an so. Ashe kun ga kenan, mu ya dace mu fi kowa son a raba ƙasar kenan. Idan aka raba ta ina za su dinga samun kayan abinci? In dai a wajen abinci ne, babu ko ja yankin Arewa shi ne yake ciyar da ƙasar. Saboda haka, Arewa ba ƙashin yadawa ba ce.

Da a ce muna yin amfani da wannan ni’imar da Allah yai mana ta ƙasar noma, ba kawai mu noma ba, mu godewa Allah ta hanyar sarrafa kayan abincin zuwa wasu nau’o’in abinci ko wasu abubuwan da ake amfani dan yin wani abinci irin su kayan maƙulashe.Tabbas da hakan ba ƙaramin ci gaba zai samar mana ba ta hanyoyi da daman gaske. Kuma Allah zai ƙara buɗa mana wasu ni’imomin da tattalin arzikinmu zai ƙara bunƙasa fiye da yanzu.

Na san wasu za su tambaya to wai ta wacce hanyoyin za a sarrafa kayan amfanin gonar? Kuma waɗanne irin abubuwa za a samar ta hanyar sarrafawar? Amsa anan ita ce, wayar da ke hannunmu ita ce amsar. Waya ba kawai dan soshiyal midiya ba, za mu iya yin amfani da ita wajen bincike dan gano yadda ake sarrafa duk wasu nau’ikan kayan abinci, domin babbar matsalar Arewa idan kuka ɗauke matsalar tsaro, ita ce matsalar rashin aiyyukan yi.

Gabaɗaya mun dogara ne da yankin kudu a kan duk kayan masarufi da kayan abincin da aka sarrafa wanda aka noma a Arewa. Masara kadai idan kuka ɗauka, za a iya sarrafa ta, ta hanyoyi ba adadi. To shiga yanar gizo, ka binciki abubuwan da za a iya yi daga masarar. Mu ‘yan Arewa tamkar zuma muke dole sai da wuta. Da yawan ba ma son yin bincike mu wahala mu gano abu da kanmu. Sai dai idan wani ya yi, mu yi sukuwar Sallah a kai. Kowa ya raja’a a kan abun har a kashe shi ya dawo ba shi da daraja.

Saboda haka, dole sai mun cire kasala, mun yi aiki tukuru. domin samun matashiya don mu zabura. Bari na kawo mana wasu ‘yan misalai. A shekarar 2014 na taɓa karaɗe duk manyan shagunan da ke Kano, har ma da Abuja. Amma an kasa samun “corn syrup” kuma fa wannan corn syrup din da masara ake yinsa. Kuma muna noman masarar sosai da sosai. Shi wannan corn syrup din ana amfani da shi sosai waje yin alawoyi iri-iri ko cakuleti, lemon kwalba, jus, nono, har ma da wani nau’in na kayan maƙulashe na gashi. Amfanin da ake da shi bazai lissafu ba.

Har ila yau za a iya sarrafa masara wajen yin corn starch, wandai ake amfani shi don yin corn syrup. Kuma ana amfani da shi ta hanyoyi da daman gaske. Wannan fa masara kenan kawai, kuma abu biyu kawai na ba da misali. Akwai abubuwa ba adadi da za a iya sarrafa masara da su. Sannan za a iya yi da yawa har matakin da za a iya fitar da wasu ƙasashe. Da a ce Arewa muna yin hakan, Wallahi ‘yan kudu ba za su dinga yi mana gori ba.

Har yanzu dai aka batun kasar noma, Idan muka ɗauki misalin gyaɗa. Duk da dai cewa ita gya]a tana cikin ahalin su wake da waken suya da sauransu. Amma idan aka ɗauke gyada da irinsu gurjiya da aya, shin a Arewa ana noman sauran abubuwan da suke da sunan “nuts” a karshe sunayensu? Misali, irin walnut, Macadamia nut, hazel nut, pine nut, alamond dss, wadannan kayan amfanin noma ne da ake noma su a wasu ƙasashen Duniya. Suna da matuƙar daraja, domin ana amfani da su ta hanyoyi bila’adadin. Zan so a ce za a gwada noman su a Arewa. Ba ƙaramin samar da kudin shiga za su yi ba. Kai! Yankin Arewa fa, Allah ya ni’imta mu, ya albarkace mu da ƙasar noma, abubuwa da yawa za a iya shuka su kuma su rayu a Arewa.

A ɓangaren dabbobi ma haka abun yake. Allah ya ni’imanta Arewa da dabbobin kiwo.abun da ya rage mana shi ne, yadda za mu inganta harkar mu zamanantar da ita kamar yadda aka zamanantar da kiwon tsuntsaye dagin Kaji da sauransu. Kamar yadda ake kiwon Kaji dan a sami kwai kawai, ko a yi kiwonsu dan nama kawai. To fa haka ma dabbobi irinsu Shanu da Awaki da Tumaki. su ma ana nomansu ko kiwonsu dan madara ko nama da sauransu. In ma akwai inda ake yi din a Arewa, za ka ga bai fi a ƙirga su ba.

Abun da ya rage mana kawai shi ne, yin bincike. Mu yi godiya ga Allah ta hanyar gano da sarrafa wannan ni’imar da Allah ya ba mu, domin har yau, har gobe daga Arewa ake kai dabbobi kudu, su ba su da wannan ni’imar sai mu.

A ƙarshe, tabbas yawan al’umma da ƙasar noma da dabbobin kiwo, duk ni’imomi ne daga Allah. Allah ya azurta yankin Arewa da su. Babban abin da ya rage mana, mu ƙara ƙokari a kan wanda muke yi yanzu wajen sarrafawa da ingantawa da kuma faɗaɗa tunaninmu akan waɗannan ni’imomin domin cigaban yankinmu da ma ƙasa bakiɗaya.

Hakan zai yiwu ne kaɗai idan a ranmu muka cire uzurin matsalar tsaro da matsalar rashin wutar lantarki, domin kuwa hakan dai wasu suke zuwa daga can wasu ƙasashen su zuba hannun jari, su bude manyan kamfanoni. Bayan mu ma muna da manyan masu kuɗi ko manyan ‘yan kasuwar da suke da arzikin da za su iya fiye da baƙin haure.

Waɗannan ni’imomin ba abubuwa ba ne da za mu yi watsi da su ba. Shi ya sa marigayi Abubakar Ladan ya ke cewa: “Bisa gaskiya ni’imar da Allah yai mana, bai kyautu mu yi watsi da su ba a duniya…”

Bashir Ibrahim Na’iya ya rubuto ne daga Baltimore a Maryland da ke ƙasar Amurka (USA)