Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Hon. Ibrahim Iliyasu, shugaban ƙungiyar wayar da kai ta siyasar matasa masoyan Sanata Barau I Jibirin da ake kira Mai Kaza Political Awarness, ya koka da roƙon DSP Barau da ya tsawatarwa jami’an tsaronsa kan yadda suke tozarta jama’a a duk wani taro na DSP kamar dai yadda ya zargi jami’an tsaron Sanata Barau sun yi masa dukan tsiya ta hanyar cakumosa a daidai lokacin da yake sauraron jawabin Sanata a ɗakin taron Ammani da aka yi a makon nan a Kano, inda suka yi masa duka bai san abin da ya musu ba.
Hakan ya ce kila dai akwai maƙiya Sanata a cikin jami’an tsaron da ke son tawarwatsa masa jama’a don biyan buƙatun iyayen gidansu na wata jam’iyyar a cewar Mai Kaza Bichi.
Ya kuma ƙara da cewa wananan matsala ta sa ya shaida wa Hajiya ‘Yardada Mai Kano, Bichi, mai bai wa Sanata shawara don ta miƙawa Sanata kokensa inda ta nuna damuwarta kan dukan mai kaza da jami’an tsaron suka yi a ƙarshe Ibrahim Iliyasu ya Mai Kaza ya bai wa DSP kan nuna kishi ga al’umar Kano da ƙasa baki ɗaya na tura ɗalaibai 70 karatu ƙasar waje, inda ɗaya daga cikin iyayen yara Egn Musubahu Rufai Gwarzo, shi ma ya ba kan sauran ‘ya’yan su karatu irinsu Mansur Rufai Waziri karatu Indiya don yin digiri na biyu.
