Tashar samaniya ta Sin: ‘Yan sama jannati na kumbon Shenzhou-14 sun fara tattaki a wajen tashar

Daga CMG HAUSA

‘Yan sama jannatin ƙasar Sin na kumbon Shenzhou-14, sun fara tattakin da aka tsara zai kai na sa’o’i 7, a wajen tashar binciken sararin samaniya ta ƙasar Sin, tun daga karfe 6:26 na yammacin Alhamis din nan, bisa agogon birnin Beijing, daidai da ƙarfe 10:26 agogon GMT.

Dan samajannti Chen Dong ne ya buɗe ƙofar fita, ta ɓangaren ɗakin binciken samaniya na Wentian dake tashar ta samaniya.

Kana Chen Dong da Liu Yang suka fita wajen ɗakin, yayin da Cai Xuzhe ke tallafa musu da wasu hidimomi ta cikin tashar.

Ana sa ran ‘yan sama jannatin za su dasa ƙarin wasu fanfuna, su kuma daga kyamara mai jujjuyawa dake saman ɗakin binciken.

Fassarawar Saminu Alhassan