Na gaba ya yi gaba….

Daga IBRAHIM YAYA

Da alamu dai haɗin gwiwar dake tsakanin ƙasar Sin da ƙasashen Afirka, tana ci gaba da tsolewa wasu ƙasashe ido, waɗanda a baya suke ta yunƙurin ƙirƙiro bayanai na ƙarya da nufin ɓata wannan alaƙa mai dimbin tasiri da fa’ida ga ɓangarorin biyu. Amma bakin alƙalami ya riga ya bushe.

Ƙasa ta baya-bayan nan da ta bijiro da maitarta a fili wajen ganin ta ƙulla alaƙa da ƙasashen Afirka, ita ce ƙasar Japan, inda ta shirya taron raya ƙasashen Afirka karo na 8 a kasar Tunusiya daga ranar 27 zuwa ta 28 ga watan Agustan shekarar 2022 da muke ciki.

A yayin taron, firaministan Japan Fumio Kishida ya sanar ta kafar bidiyo cewa, a cikin shekaru 3 masu zuwa, ƙasarsa za ta zuba jarin Dala biliyan 30 a ƙasashen Afirka, sannan za ta horas da ƙwararrun nahiyar dubu 300 da dai sauransu.

A cewarsa wai, “Wannan aiki ya sha bamban da na ƙasar Sin”.

Amma, idan mutum ya ce zai ba ka riga, aka ce ka kalli ta wuyansa.
Idan har Japan da sauran ƙasashen yamma suna son su rudi ƙasashen Afirka da sunan tallafi ko horas da ƙwararru, don kulla wata alaka ta moriyar kansu, ya kamata su san cewa, ƙasashen Afirka sun dade suna kuma ci gaba da amfana da haɗin gwiwarsu da ƙasar Sin.

Wannan dai wani salo ne na wayon a ci, wai an kori kare daga gindin ɗinya. Amma kan mage ya waye.

Ai ko bayan Japan da wasu ƙasashe, ita ma ƙasar Amurka ta shelanta irin wannan alƙawari mai kama da romon baka, yayin taron G7 da ya gudana a ƙasar Jamus a wani lokaci cikin wannan shekara, inda ta yi iƙirarin kafa wata gidauniya da sunan tallafa wa ƙasashe masu tasowa, duk da neman ɓata sunan shawarar “ziri ɗaya da hanya ɗaya” da ƙasar Sin ta gabatar.

Koma dai mene ne, abin tambaya shi ne, me ya sa sai yanzu ƙasar Japan da sauran ƙasashen yamma ke neman ƙulla alaƙa da ƙasashen Afirka, bayan da Sin da Afirka suke ƙara cin gajiyar alaƙarsu mai cike da aminci da mutuntawa da kare moriyar juna a dukkan sassa?

Kifi dai yana ganin ka mai jar koma. A yi dai mu gani, idan har tusa tana hura wuta.