Tashin hankali: ISWAP ta fitar da bidiyon kashe sojojin Nijeriya a Yobe

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kungiyar da ke samun goyon bayan ƙungiyar Boko Haram, ISWAP, wadda a da ake kira Jama’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihad, ta fitar da wani faifan bidiyo da ke nuna yadda aka kashe wasu sojojin Nijeriya uku.

A wani ɓangare na faifan bidiyon, maharan sun harbe sojojin ne da bindigogi. A cewar rahotanni, lamarin ya faru ne a ranar 15 ga Maris, 2025 a jihar Yobe. An ce an kama sojojin ne a yankin Kamuya da Azare na jihar. Bidiyon ya nuna mutanen uku sun durƙusa a wani fili suna gabatar da kansu a matsayin jami’an tsaron Nijeriya kafin wasu mutane da suka rufe fuskokinsu suka buɗe musu wuta.

Tun bayan rasuwar shugaban JAS, Abubakar Shekau, ƙungiyar ISWAP ke ƙara ƙarfafa gwiwa a yankunan da ke kusa da tafkin Chadi. Mambobin ƙungiyar sun watsu tare da sauya sheƙa na ɗaruruwan mayaƙan Boko Haram ƙaraashin Shekau.

Rundunar sojin Nijeriya ta sha yin ikirarin cewa an yi galaba a kan ‘yan ta’addan kuma a lokuta da dama suna yin watsi da labari na haɗari a kan ƙungiyar. ƙungiyar ta’addanci ta yi sanadin mutuwar sama da 100,000 tare da raba miliyoyin mutane da muhallansu musamman a jihohin Adamawa, Borno da Yobe.

A wani labarin kuma, wasu mayakan aungiyar ISWAP da dama sun miƙa wuya ga jami’an tsaro a jihar Borno sakamakon munanan hare-hare ta sama da rundunar sojin saman Operation Hadin Kai (OPHK) da hadin gwiwar sojojin Nijar suka yi.

Wata majiyar leƙen asiri ta shaidawa Zagazola Makama a ranar Larabar da ta gabata cewa, an kai harin ne a ranar 17 ga watan Maris a Chettimari da ke kan iyaka a Jamhuriyar Nijar, kusa da Damasak a jihar Borno.

Hare-haren na ta’addancin da aka kai kan mayakan ISWAP bayan sun kai wa sojojin Nijar hari, sun kashe sojoji aƙalla huɗu tare da jikkata wasu bakwai.

Sai dai a cikin gaggawar shiga tsakani, dangane da kiran da aka yi daga makwabciyar kasar, rundunar sojojin saman Nujeriya ta tura Super Tucano guda biyu, wadanda ke samun goyon bayan bayanan sirri, sa ido, da kuma binciken kadarorin (ISR) daga jamhuriyar Nijar, inda suka yi wa ‘yan ta’adda mummunar barna tare da dakile ayyukansu.

“Sakamakon harin da a ka kai ta sama, mayaaan ISWAP da dama sun mika wuya a jihar Borno da makamansu da dawakai,” inji majiyar.