Boko Haram ke da alhakin kashi 66 na yawan tashe-tashen hankula a Nijeriya – Rahoto

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

ƙungiyar Boko Haram da ISWAP ne ke da alhakin  kashi 66 cikin 100 na duk wani tashin hankali da aka samu a Nijeriya a shekarar 2024, a cewar wani sabon rahoto da Cibiyar Nazarin Dabarun Afirka (ACSS) ta fitar.

Rahoton ya bayyana cewa tashe-tashen hankulan masu tsattsauran ra’ayi a yankin tafkin Chadi, da ƙungiyar Boko Haram da ISWAP suka haddasa, ya yi sanadiyar mutuwar mutane 3,627, wanda ya sa yankin ya zama na uku mafi muni da tashe-tashen hankula a Afirka, bayan Sahel da Somaliya.

Arewa maso Gabashin Nijeriya: Cibiyar tashe-tashen hankula:

Duk da raguwar mace-mace da kashi 4 idan aka kwatanta da shekarar 2023, yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya ya kasance cibiyar tashe-tashen hankula masu nasaba da Boko Haram. Rahoton na ACSS ya yi nuni da cewa, Boko Haram da ISWAP, duk da cewa sau da yawa suna rikici da juna, sun faɗaɗa ayyukansu zuwa arewacin Kamaru, lamarin da ya kai kashi 51 cikin 100 na tashin hankali a can.

A karon farko, Kamaru ta sami rahotannin tashe-tashen hankula masu alaƙa da Boko Haram fiye da Nijeriya, inda aka samu afkuwar al’amura 711, idan aka kwatanta da na Nijeriya 592.

Masana harkokin tsaro sun yi gargaɗin cewa hare-haren da Boko Haram da ISWAP ke ci gaba da yi a kan iyakokin ƙasar na haifar da mummunar barazana a yankin, wanda ke kawo cikas ga ƙoƙarin sojojin Nijeriya da na Kamaru. Duk da ci gaba da ƙoƙari soji, waɗannan ƙungiyoyin sun daidaita dabarunsu, wanda hakan ya sa hukumomin tsaro ke da wuya su shawo kan tashe-tashen hankulan.

Bayan tafkin Chadi, rahoton ya nuna cewa yankin Sahel ya kasance yankin da ya fi fama da tashin hankali a cikin shekara ta huɗu a jere, wanda ya kai kashi 55 na yawan mace-mace masu alaƙa da Boko Haram a nahiyar, inda aka yi kiyasin mutuwar mutane 10,400 a shekarar 2024.

Wannan tashin hankalin dai ya samo asali ne sakamakon hare-haren ta’addanci daga ƙungiyar IS a Sahel (IS Sahel) da ƙungiyar Jama’at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM) mai alaƙa da al-ƙaida.

Burkina Faso ita ce ta fi fama da matsalar, wadda ke da kashi 61 na yawan mace-macen masu alaƙa da masu ikirarin jihadi a yankin Sahel. A watan Satumba, JNIM ta kai hari ɗaya daga cikin mafi muni a shekarar, inda aka kashe mutane kusan 400 a garin Barsalogho na ƙasar Burkina Faso.

Yayin da yankin Sahel da tafkin Chadi ke ci gaba da fuskantar tashe-tashen hankula, Somaliya ta samu raguwar kashi 41 cikin 100 na mace-macen masu alaƙa da masu ikirarin jihadi a shekarar 2024, inda aka samu rahoton mutuwar mutane 4,482. Ana danganta wannan da ayyukan al-Shabaab, duk da keɓantattun hare-hare kamar harin da aka kai a gaɓar tekun Mogadishu wanda ya kashe mutane 32.

Jaridar Le Monde ta nakalto Abdifatah Adan Hassan mai magana da yawun ‘yan sandan Somaliya yana cewa “Kai hari da bama-bamai na kashe mutane 32 daga cikin fararen hula na nufin waɗannan Khawarijawa ba za su kai hari kan cibiyoyin gwamnati, sojoji da jami’ai kawai ba. Jami’an Somaliya na amfani da kalmar Kharijites wajen bayyana mayaƙan al-Shabaab.

Duk da bambance-bambancen yanki na tashe-tashen hankula na ‘yan bindiga, manazarta harkokin tsaro sun yi gargaɗin cewa ci gaba da ayyukan Boko Haram da ISWAP a Nijeriya da kuma ƙasashen da ke makwabtaka da ita na da matuƙar tayar da hankali.