Tasirin abokai da ƙawaye

Spread the love

Tare da BILKISU YUSUF ALI

Idan aka ambaci kalmar “aboki” ga namiji,  abin da yake fara zuwa a tunanin mutane shine, wani tsayayyen masoyi wanda kanwarku ke jiƙo wuri guda da shi. Wanda kuma bayan so da yake maka, yana sahun gaba na masu burin ci gabanka da kuma son ganin ka zauna lafiy      a, a gida da waje. Kamar haka kuma yake idan ka ambaci “ƙawa” ga mace. Ko wace rawa abokai da ƙawaye suke takawa a cikin zaman aurenmu?

A cikin kowane motsi da dukkan harkokin da mutum zai yi, bayan ya zama baligi, za ka taras ya fi sakin jiki da abokai ko ƙawayensa. Don haka suna sanin sirrikan juna fiye da iyayensu. Saboda mun fi jin junanmu a wani mataki iri ɗaya, wanda da zarar mun yi magana za mu fahimci juna.  Wannan yanayin kuma shi ya sa abokai da ƙawaye suke da matuƙar muhimmanci a cikin zamantakewarmu da iyali. Kai tsaye ma dai wasu masana suna ganin ana iya auna  nasara ko rashin nasarar zaman auren mutum bisa la’akari da irin abokan da yake da su, ko ƙawayen da take da su. Abu mafi tayar da hankali yanzu, shi ne yadda abokai da ƙawaye suke taka muhimmiyar rawa wurin rusa aure. 

Me ya sa abokai da ƙawaye suke tasiri? 

Masana ɗabi’un ɗan’adam suna cewa, ɗaya daga cikin hanyoyin da mace take samun sauƙin yayin da ta shiga cikin damuwa, shi ne ta haɗu da wata ƙawarta su tattauna game da wannan matsalar. Ta zayyana duk abin da ya dame ta. Ko kuma su bayyana wa juna dukkan matsalolinsu. Wani lokacin har su yi koke-koke, a yi hoho-juna, sannan su rabu. Kuma daga lokacin sai kowaccensu ta ji ta sami sauƙin abin da ke damunta. Kuma su ma maza, ko da yake an bayyana cewa su ba su cika bayyana matsalar zamantakewarsu ga mutum ba sai dai wanda suke sa ran idan sun bayyana mar din, yana da shawarwarin da zai iya ba su. Amma hakan ba ya nufin ba sa bayyanawa kwata-kwata. Maza ma sukan tattauna matsalolin zamantakewarsu da abokai, sai dai a ce ba kamar  mata ba. 

Yayin da kuwa mutum ya buɗe sirrinsa ga wani, to babu ko shakka abu ɗayan uku zai iya faruwa. Ko dai ya taimaki zamantakewarka  idan mutumin kirki ne, ta hanyar kwantar ma da hankali da ba ka shawarwari nagari. Ko ya gurɓata ta, ta hanyar ƙara tunzura ka da ba ka miyagun shawarwari. Ko kuma dai idan ya kasance mai taka-tsantsan da ƙarancin kutse, ya ba ka haƙuri ba tare da wata shawara ba.  Yayin da mutum ya yi rashin sa’a, ya haɗu da aboki ko ƙawa maras kirki kuwa, babu shakka rayuwar aurensa takan sha wahalar gaske. Domin a ko da yaushe dai, yayin da ka ga mutum ya zauna ya buɗe maka sirrika da matsalolinsa, ko shakka babu hakan yana nuni ne da cewa maganarka ko hangenka da za ka tofa a cikin sha’anin yana da matukar tasiri a wurinsa ne. Don haka abu ne mai sauki ɗora wanda yake cikin irin wannan yanayi a turba sahihiya ko kuma rufta shi a rami.  

A mafi yawan lokaci, ba wai sai wawa ko maras ilimi ake yi wa ingiza mai kuntu ruwa a irin wannan lokaci ba. Akan iya yi wa kusan kowanne irin mutum. Domin abin yakan yi kama da ha’inci ne. Akan sakankance da mutum ne saboda amincin da ke tsakani, sam ba a tsammanin zai kawo wata mugunyar magana ko gurguwar shawara. Don haka yana faɗar magana, musamman a lokacin da rai yake a ɓace, sai kawai a ɗauka, a aiwatar. Sai daga baya in mutum ya dawo hayyacinsa, ya cika da nadama.  Wata Bazawara da na tattauna da ita ranar talatar da ta gabaga, ta shaida min cewa. Watarana ta je gidan ƙawarta da suke ƙut tana gaya mata matsalolin mijinta. Sai ta ce mata “Ai mijinki ya ban mamaki. Kwanaki fa da mijina yana yi mar nasiha, ya ce mar ya kamata ya dena yi miki rashin mutumci, ko dan kar shi ma a yi wa ‘yarsa in ta girma. Sai ya ce wai a yi mata ɗin mana, ina ruwansa!” Ita kuwa daga jin wannan magana sai ta ƙara tunzura, ta je ta yi wa miji wankin babban bargo. Ta ƙara da cewa ƙawar nan ba ta gushe ba tana ce mata ya yi kaza ya ce kaza, kamata ya yi ke ma ki yi kaza, in ba haka ba ba zai dena ba. Har sai da wannan auren ya mutu!  Kuma daga baya da maganganun su ka bayyana sai ga shi mijin ya yi rantsuwa da abin da zai kashe shi cewa shi sam ba a ma taɓa yin magana makamanciyar wannan da shi ba!  

Duk da cewa irin wannan aɗifa ta saurin yarda da zuga ko gurguwar shawara ta fi yawa ga mata, amma hakan ba ya nufin mazan ma ba sa karɓa. A lokaci da dama akan idan abokinka ya kasance irin mutanen nan ne masu son tofa albarkacin bakinsu a cikin komai, to tabbas duk lokacin da kai sake ka gaya mar wani abu game da zamantakewarka da iyali, to tabbas ba zai rasa yin tsokaci ba. Kuma a cikin wannan tsokacin ne zai shigo da nasa ra’ayin, wanda ba lallai ne idan ka bi shi lamarin ya haifar maka ɗa mai ido ba. Domin ita harka ta zamantakewa musamman ta aure, tana bukatar ƙwararren mutum ne. Wato wanda ya daɗe a cikin rayuwa irin ta aure, kamar dattawan da ke kusa da kai. Ko kuma dai wanda yake da wani ilimi a fannin, wato masani game da ɗabi’ar ɗan’adam da hanyoyin 

warware rikici, ko mashawarci a kan zamantakewa da makamantansu. Amma ba zai yiwu kawai ka sami aboki don kana ganin wani ustazu ne, ko kuma wani gwanin iya tsara magana ne, ka ce wai shi ne zai ba ka shawarar yadda za ka tafiyar da rayuwarka da iyali. Alhali shi bai shiga wannan rayuwa ta zaman aure ba, ko kuma dai ya shiga amma yana daf da gaɓa ne, bai yi nisa ba tukum. Domin mutumin da yake a marhala ta ɗokin juna da iyalinsa, ba ya iya fahimtar ainishin yadda zaman yake.sami bayan kwana biyu, yayin da a hankali ya tsallaka marhala ta sabo da juna zuwa matakai na gaba.

By ukarofi