Tattalin arzikin Nijeriya na cikin mawuyancin hali – Shettima

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya amince da cewa a halin yanzu tattalin arzikin Nijeriya na cikin mawuyanci hali.

Sai dai ya jaddada cewa wannan matsala ba Nijeriya kaɗai ke fuskanta ba, don haka ya buƙaci ‘yan ƙasar da su marawa shugaba Bola Tinubu baya kan shawo kanta.

Shettima ya bayyana haka ne a yayin wani taron kwana ɗaya da ƙungiyar ba da damar kasuwanci ta ƙasa (PEBEC) ta shirya a Abuja ranar Juma’a.

Ya ce, “Dole ne mu haɗa kai da Shugaba Tinubu a wannan mawuyacin lokaci. Haƙiƙa tattalin arzikinmu yana fuskantar matsaloli, amma wannan ba lamari ne da ya keɓanta da Nujeriya ba. Dukka duniya ke fuskantarsa. “

Shettima ya cigaba da cewa, “Babu wani tattalin arziki da ya keɓe daga ƙalubalen wannan zamani. Yana da muhimmanci a goyi bayan shugaban ƙasa kuma mu kasance masu adalci a cikin al’amuranmu. Nasarar duk wani ci gaban tattalin arziki yana da tasiri sosai ta hanyar ingancin gyare-gyare da ke haifar da damammaki ga kasuwanci.”

By ukarofi