Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Dangane da yanayin da duniya ke ciki, NIjeriya na fuskantar hauhawar farashin kayayyakin abinci da ba a tava yin irinsa ba.
Binciken da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya ya fitar a jihohin Kaduna, Kano da Katsina ya nuna cewa ba bar Nijeriya a baya ba.
Misali, wani bincike da NAN ta gudanar a Kaduna ya nuna cewa an samu qaruwar farashin shinkafa, biredi, sikari, garri, naman sa da kwai da dai sauran su, waxanda su ne ginshiqin abinci a gidaje.
Haka nan, hauhawar farashin ya yi tasiri a rayuwar yawancin gidaje, domin kuwa yanzu suna fuskantar qalubalen samun damar cin abinci sau uku a rana.
NAN ta kuma tattaro daga babban kasuwar Abubakar Gumi da sauran kasuwannin cikin garin Kaduna cewa farashin shinkafar Mama Gold ya tashi zuwa kusan Naira 75,500 kan kowace buhu, yayin da kasuwar Stallion, Optimum mai nauyin kilogiram 50 ake sayarwa daga N77,000 zuwa N80,000.
Haka kuma, a yanzu ana sayar da biredi tsakanin Naira 1,000 zuwa Naira 2,500 dangane da nau’insa da ingancinsa.
Mudu na farin garri da ake sayarwa a kan N400 yanzu ana sayar da shi tsakanin N1200. yayin da da ake sayar da garri mai kalar ruwan kwai a kan Naira 600 yanzu a da, yanzu ya kai tsakanin N1300 zuwa N1,500.
Hakazalika, Kiras xin kwai da ake sayar da shi a kan Naira 3000 a yanzu, ana sayar da shi tsakanin N4,000 zuwa N4,500 gwargwadon girmansa a halin yanzu.
Haka kuma, kilon nama sa da a da ake sayarvda shi a kan Naira 3,000, yanzu ana sayar da shi kan Naira 5,000.
A halin da ake ciki, manoma a sassan jihar sun danganta tsadar kayan abinci da cire tallafin man fetur.
Wasu daga cikin manoman da suka zanta da NAN a wata tattaunawa daban-daban a garin Kafanchan, sun xora alhakin tashin farashin kayan abinci a kan tsadar sufuri, lamarin da ya biyo bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi.
Wani babban manomi mai suna Ishaya Chingali ya ce hauhawar farashin kayayyaki ya kuma haifar da tsadar kayan noma kamar takin zamani maganin ciyawa.
“Idan za su kawo kan farashin sufuri, za a magance tsadar kayan abinci da kashi 50 cikin xari,” inji shi.
A nasa vangaren, shugaban qungiyar manoman Citta, Kure Kade, ya ce mafita kawai ita ce gwamnati ta ba da tallafin kayan amfanin gona.
Ya ce; Nijeriya na iya ciyar da kanta ba tare da an shigo da kayan abinci daga waje ba.
A wani labarin makamancin haka, gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta raba kayan noma da na’urorin noma da kuma na’urorin sarrafa amfanin gona ga qananan manoma 40,000 domin bunqasa noman abinci.
Murtala Dabo, kwamishinan ma’aikatar noma ne ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya a Kaduna.
An raba kayayyakin ne a qarqashin shirin gwamnati na ‘A Koma Gona’ (Back to Farm).
A cewarsa, shirin ya shafi waxanda suka ci gajiyar tallafin a qananan hukumomi 23 na jihar.
Ya ce; jihar ce kan gaba wajen noman citta da masara da kuma tumatur a qasar nan, inda ya koka kan yadda manoman suka yi asara bayan girbi irin su tumatur da citta.
Aminu ya yaba wa gwamnatin tarayya bisa tallafin kayan noman rani ta hanyar shirin bunqasa noma na qasa da kuma Agro Pocket (NAGS –AP).
Sai dai ya buqaci gwamnati da ta ci gaba da bunqasa shirin na qarfafa samar da abinci da ayyukan yi.
A cewarsa, NAGS-AP na xaya daga cikin shirye-shiryen gwamnati mafi kyau da ke yi wa qananan manoma tagomashi, ta yadda za a inganta samar da abinci.
Nuhu Aminu, shugaban qungiyar manoma ta Nijeriya (AFAN) reshen jihar Kaduna, ya danganta tsadar kayan abinci a jihar da rashin isassun kayan aikin noma da kuma jinkirin noma.
Aminu ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya a Kaduna.
Ya bayyana cewa manoman ba sa iya fara noma da wuri ko da damina saboda tsadar takin zamani da rashin rarraba iri da magungunan kashe kwari da dai sauransu.
