Tattalin arzikin Nijeriya na samun tagomashi – Tinubu ga taron ƙungiyar Editoci

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cewa sannu a hankali tattalin arzikin Nijeriya na samun tagomashi, yana mai alaƙanta ci gaban da aka samu da sauye-sauyen da gwamnatinsa ke aiwatarwa a sassa daban-daban.

Shugaban ya bayyana haka ne a garin Yenagoa na jihar Bayelsa a ranar Alhamis a jawabinsa na buɗe taron Editocin Nijeriya.

Yayin da ya ke magana ta bakin ministan yaɗa labarai da wayar da kai na Nijeriya, Mohammed Idris, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa ya kwashe watanni goma sha takwas yana kafa harsashin manufarsa ta samar da ci gaban Nijeriya.

Ya bayyana cewa, sakamakon gyare-gyaren da aka yi, kuɗaɗen shiga na dukkan matakai uku na gwamnati – Tarayya, Jihohi, da ƙananan Hukumomi – ya samu bunƙasa sosai, wanda hakan ya ba da damar saka hannun jari a fannin ayyukan jin ƙai, samar da ababen more rayuwa, da samar da zaman lafiya.

Shugaban ya bayyana cewa kotun ƙoli ta yanke hukuncin bai wa ƙananan hukumomi ’yancin cin gashin kansu, biyo bayan ƙarar da gwamnatin tarayya ta shigar, na da nufin ƙarfafa harkokin mulki a matakin ƙananan hukumomi da kuma samar da ci gaban ƙasa.

Ya jaddada ƙudurin sa na ganin ba a bar wani ɗan ƙasa a baya ba cikin talauci.

“An fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 a dukkan ma’aikatun Gwamnatin Tarayya, inda da yawa daga cikin gwamnatocin jihohi suka ƙuduri aniyar aiwatar da hakan. Sama da ɗalibai 46,000 ne ke cin gajiyar asusun ba da lamuni na ilimi na Nijeriya a faɗin manyan makarantu 59 tare da kashe sama da Naira biliyan 5. Kashi na farko na ma’aikatan gwamnati 500,000 za su ci gajiyar shirin bayar da lamuni na masu amfani da shi tare da fitar da naira biliyan 100.

Ya ce, kowane ɗaya daga cikin tsare-tsaren an tsara shi ne domin ya zama wani shiri da zai samar da ci gaba mai ɗorewa a rayuwar miliyoyin ‘yan Nijeriya.

Yayin da yake yaba wa kafafen yaɗa labarai kan sadaukar da kai ga gina ƙasa, musamman wajen tallafa wa dimokraɗiyyar Nijeriya mai ɗorewa, Shugaba Tinubu ya jaddada cewa ayyukan gwamnati da na kafafen yaɗa labarai na da alaƙa da juna, dukkansu suna da matuƙar muhimmanci wajen biyan buƙatun jama’a.

By ukarofi