TikTok ya gamu da cikas

Daga BASHIR ISAH

A safiyar ranar Alhamis dandalin TikTok ya gamu da cikas, lamarin da ya jefa dubban masu amfani da manhajarsa a faɗin duniya cikin mawuyacin hali.

A cewar shafin intanet na DownDetector mai bibiyar ire-iren waɗannan batutuwa, matsalar ta fara ne da misalin ƙarfe 09:40 agogon GMT daidai da ƙarfe 04:40 agogon ET.

Ya zuwa haɗa wannan labari, kimanin mutum 3,000 sun shigar da ƙorafi rashin aikin manhajar TikTok mallakar wani kamfanin Chana mai suna ByteDance.

Masu amfani da manhajar a sassan duniya, ciki har da mazauna Birtaniya da London, ne suka yi ƙorafi kan matsalar da aka fuskanta da TikTok.

Kawo yanzu, kamfanin TikTok bai ba da dalilin aukuwar matsalar da aka fuskanta game da manhajar ba.