Tinubu bai je Faransa domin duba lafiyarsa ba – Fadar Shugaban ƙasa

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Mai ba da shawara ga shugaban ƙasa, Daniel Bwala, ya ƙaryata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na ƙasar Faransa domin neman magani.

A cewarsa, shugaba Tinubu yana ziyarar aiki ne, ba don jinya ba. “Wasu lokuta a dandalin sada zumunta sai ka ga wani yana yaɗa labari, wanda ba ma ka san ko wanene ba. Wata kila yana da matsala ta ƙwaƙwalwa,” in ji Bwala yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a tashar Channels Television.

Tinubu ya bar Najeriya a ranar 2 ga Afrilu, 2025, zuwa birnin Paris na ƙasar Faransa, inda mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa ziyarar aiki ce da za ta taimaka wajen nazarin ci gaban manufofin gwamnati da kuma tsara shirye-shiryen da suka shafi zagayowar shekara ta biyu ta gwamnatin Tinubu.

A wani faifan bidiyo da fadar shugaban ƙasa ta wallafa, an ga Tinubu yana gaisawa da manyan jami’an gwamnati kafin ya hau jirgin fadar shugaban ƙasa.

Fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa shugaba Tinubu zai dawo gida Najeriya kafin ko a ranar 16 ga Afrilu, 2025.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da ake ci gaba da samun rahotannin da ba su da tushe a kafafen sada zumunta. Gwamnati ta buƙaci ‘yan ƙasa da su riƙa tantance sahihancin labarai kafin yaɗa su.

By ukarofi