Tinubu: Kansilolin APC sun ba Baba-Ahmed awa 48 ya janye kalamansa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gamayyar Kansilolin Jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya ta bai wa mataimakin ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar Labour, Datti Baba-Ahmed awanni 48 ya janye kalamansa kan batun cewa gwamnati ta dakatar da rantsar da zavavven Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinibu ba a 29 ga Mayun 2023 mai zuwa.

Gamayyar Kansilolin na APC sun bayyana cewa za su ɗauki matakin shari’a matuƙar Datti Baba-Ahmed bai fito ya janye kalamansa ba kuma ya nemi yafiyar ‘yan Nijeriya.

Idan za a iya tunawa, shi ma Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu na Nijeriya, Alhaji Lai Mohammed ya zargi ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, da tada hankalin jama’a kan sakamakon zaɓen shugaban ƙasa, yana mai cewa cin amanar ƙasa ne abin da yake yi.

Obi ya zo na uku a zaɓen shugaban ƙasa da aka yi ranar 25 ga watan Fabrairu wanda Bola Tinubu na jam’iyyar APC mai mulki ya lashe. Shi Obi da Atiku Abubakar da ya zo na biyu, suna ƙalubalantar sakamakon zaɓen a kotu, inda suka ce zaɓen da kuma sakamakon zaɓen ba abin da mutane suka zaɓa ba ne aka bayyana. 

Dukkan ‘yan takarrar biyu sun fito fili sun yi kira ga magoya bayansu da su guji tashin hankali yayin da suke ƙalubalantar sakamakon a kotu.

Sai dai kuma musamman magoya bayan Obi sun ci gaba da nuka ɓacin ran su bisa ga sakamakon zaven suna masu cewa suna nan a bakansu na dole a dakatar da rantsar da Bola Tinubu Shugaban Ƙasa ranar 29 ga Mayu.

”Bai kamata a ce wai Obi da mataimakin sa Datti su riƙa furta kalaman da su tada hankalin ‘yan Nijeriya ba, su riqa cewa idan aka rantsar da Tinubu Dimokuraɗiyya a Nijeriya ta zama gawa ba.

“Irin kalaman da Obi ke furtawa kalamai ne na mutumin da ya sha kayi. Amma A ina ake baiwa wanda ya zo na uku shugabanci bayan ga na ɗaya da na biyu idan ba Obi da maqarrabansa sun zauce ba.

A ƙarshe Lai Mohammed ya ce ya ziyarci Amurka ne domin ya wayar musu da kai game da ƙarerayin da suke ji suke kuma yaɗawa game da zaven Nijeriya.

Mafi yawa daga cikin ‘yan Nijeriya sun amince cewa zaven 2023 ya fi zaɓukan da aka taɓa yi a Nijeriya tun 1999.