‘Yan bindiga sun sace mutum 60 a Zamfara da Katsina

‘Yan bindiga sun sace mutum 60, galibinsu ƙananan yara, a ƙauyukan da ke kan iyakar jihohin Zamfara da Katsina.

Manhaja ta kalato cewar waɗanda lamarin ya shafa sun fito ne daga ƙauyukan Kucheri da Wanzamai da kuma Danwuri da ke cikin Ƙaramar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara da garin Yankara a yankin Ƙaramar Hukumar Faskari a Jihar Katsina.

Lamarin ya auku ne a ranar Juma’a yayin da ‘yan bindigar suka fito daga Dajin Sububu a Jihar Zamfara zuwa dajin Birnin-Gwari a Jihar Kaduna.

Duk da dai babu wani bayani a hukumance daga ‘yan sandan yankin, amma bayanai sun ce ‘yan bindigar na yin ƙaura daga Zamfara ne sakamakon matsin lambar da suke fuskanta daga sojoji inda aka kashe musu ‘yan uwa sama da 100 a cikin mako guda

Wani mazaunin Tsafe mai suna Ahmad Kucheri, ya shaida wa jaridar News Point Nigeria cewar, ‘yan bindigar kan yi awon gaba da duk waɗanda suka gani a hanyarsu ta tserewa daga jihar.

Ƙoƙarin da aka yi domin jin ta bakin Kakakin ‘yan sandan jihar, CSP Mohammed Shehu, ya ci tura.