Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa sabuwar cibiyar Kwalejin ‘Yan Sanda ta Nijeriya a Erinja, ƙaramar Hukumar Yewa ta Kudu a Jihar Ogun, tare da ware Naira biliyan 15 a matsayin kudin fara aikin gina cibiyar.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar, inda ya ce wannan mataki ya yi daidai da dokar kafa Kwalejin ‘Yan Sanda ta shekarar 2021, wacce ta bai wa makarantar damar bude rassan karatu a sassa daban-daban na ƙasar nan.
Sanarwar ta bayyana cewa kuɗin da aka ware za a samo su ne daga asusun TETFund na shekarar 2026, inda za a yi amfani da su wajen gina muhimman abubuwa kamar gine-ginen makaranta, dakunan kwanan dalibai, kayayyakin horo da sauran abubuwan da ake bukata domin fara aiki a sabuwar cibiyar.
An ce shawarar kafa wannan sabuwar harabar a Erinja ta samo asali ne daga wani babban taron tuntuba da ya hada da Ministan Harkokin ‘Yan Sanda, Ministan Ilimi Dr. Tunji Alausa, jami’an Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, da kuma sakataren Hukumar Jami’o’i ta Kasa (NUC), inda suka duba batutuwan da suka shafi daukar dalibai, kudade, ingancin ilimi da kuma buƙatar karin horo ga rundunar ‘yan sanda.
Fadar Shugaban ƙasa ta ce Tinubu na ganin cewa fadada Kwalejin ‘Yan Sanda zai taimaka wajen inganta tsarin shugabanci, koyar da aikin ‘yan sanda na zamani da kuma karfafa tsaron kasa baki daya.
A baya dai Kwalejin ‘Yan Sanda ta Nijeriya na da haraba guda daya ne kawai a Wudil, Jihar Kano. Sai dai dokar ‘yan sanda ta bai wa makarantar damar kafa karin harabobi a sassa daban-daban na kasa bisa amincewar Hukumar Jami’o’i ta Kasa.
Tun a watan Yunin 2025 ne Majalisar Wakilai ta bukaci a raba ayyukan Kwalejin zuwa yankuna daban-daban na kasar nan, inda ta roki shugaban kasa da kwamitin gudanarwa na makarantar su tabbatar da kafa haraba a kowanne yanki daga cikin yankuna shida na Nijeriya.
Kwalejin ‘Yan Sanda ta fara aiki ne tun shekarar 1988 a wasu wurare na wucin gadi a Kano da Kaduna, kafin daga bisani a hade ta zuwa Wudil a 1996. A shekarar 2012 kuma, Hukumar Jami’o’i ta Kasa ta ba ta damar bayar da digiri, lamarin da ya mayar da ita daya daga cikin jami’o’in gwamnatin tarayya.
A halin yanzu makarantar na bayar da shirye-shiryen karatu na digiri da na gaba da digiri a fannoni daban-daban da suka hada da dokokin tsaro, kimiyya, zamantakewa da gudanarwa.
Sabon harabar da za a kafa a Jihar Ogun shi ne na farko daga cikin sabbin rassan da za a bude karkashin dokar shekarar 2021.
