Tinubu ya bada umarnin amfani da jirgin sama domin kare Injiniyoyin da ke gyaran layin lantarki na Kaduna-Shiroro

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna damuwa kan rashin wutar lantarki a arewacin Najeriya da aka yi tsawon sati guda, yayin da gwamnatin tarayya ta tabbatar da ƙoƙarin samar da tushen wutar lantarki na daban don magance matsalar.

An samu matsalar ne sakamakon lalata layin wutar lantarki na Shiroro-Kaduna, wanda ya jefa yankin cikin duhu na tsawon kwanaki. A sakamakon haka, shugaba Tinubu ya kira ministan lantarki Adebayo Adelabu, da Mashawarcin tsaro na Ƙasa, Malam Nuhu Ribadu, don tattaunawa kan matsalar. Shugaban ya umarci NSA ya baiwa injiniyoyin da ke gyaran layin wutar kariya. Ya buƙaci sojin sama su bada kariya da jirgin sama domin injiniyoyin su kammala aikinsu cikin natsuwa babu fargaba.

A wata sanarwa da kakakin shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya fitar, ya ce Tinubu ya nuna baƙin cikinsa kan yadda ake yawan samun lalacewar kayan lantarki, yana mai bada umarni ga Ministan Lantarki da sauran hukumomi su gaggauta dawo da wutar. Ya kuma buƙaci al’ummar yankin da shugabanni su bada goyon baya wajen kare kadarorin gwamnati daga lalata su.

Bayan ganawar, Minista Adelabu ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na shirye-shiryen samar da tushen wutar lantarki ta daban ga jihohin arewa domin rage tasirin rashin wutar. Adelabu ya ce ana amfani da tashar Ikot Ekpene da aka samar daga Calabar don samar da wutar a arewa.

Haka zalika, gwamnonin arewa da sarakunan gargajiya sun nuna damuwarsu kan yadda rashin wutar ya ƙara jefa jama’ar yankin cikin wahala, kamar yadda aka tattauna a taron gaggawa na Ƙungiyar gwamnonin Arewacin Nijeriya (NSGF) a Kaduna.

Ƙungiyar Arewacin Nijeriya (ACF) ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar rashin wutar a Arewa, tana mai gargaɗin cewa rashin wutar yana da hatsari ga tsaron yankin da tattalin arzikinsa.

Haka shima, Kakakin majalisar dokoki na Jihar Kano, Jibril Ismail Falgore, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta hanzarta magance matsalar. Ya jaddada buƙatar samar da tushen wutar lantarki na daban don rage cunkoson da ake samu a kan layin ƙasa da tabbatar da cigaban tattalin arziki mai ɗorewa.