
Shugaba Bola Tinubu ya amince da naɗa tsohon shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Mahmud Yakubu, a matsayin jakadan Nijeriya a kasar Ƙatar.
Haka kuma shugaban kasar ya tura tsohon minista, Femi Fani-Kayode, a matsayin jakadan Nijeriya a Jamus, yayin da ya nada Aminu Dalhatu jakadan Nijeriya a Birtaniya.
Bayanin hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar a ranar Juma’a.
Rahotanni sun nuna cewa Majalisar Dattawan Najeriya ta riga ta tabbatar da sunayen jakadun tun a watan Disambar da ya gabata, kafin daga bisani shugaban kasar ya amince da kasashen da za a tura su domin wakiltar Nijeriya.
Daga cikin jerin jakadu 34 da aka amince da su akwai tsoffin gwamnoni, ministoci da manyan jami’an gwamnati.
Wasu daga cikinsu sun hada da Grace Bent (Togo), Ita Enang (Afirka ta Kudu), Victor Ikpeazu (Spain), Nkechi Linda Ufochukwu (Isra’ila), Paul Oga Adikwu (Vatican City), Ibok-Ete Ekwe Ibas (Philippines), Reno Omokri (Mexico) da Abasi Braimah (Hungary).
Sauran sun hada da Angela Adebayo (Portugal), Olumilua Ayotunwa (Japan), Ifeanyi Ugwuanyi (Greece), Chioma Ohakim (Poland), Abdulrahman Bello Dambazau (China), Tasiu Musa Maigari (Gambia), Olufemi Pedro (Australia) da Muhammed Ubandoma Aliyu (Argentina).
Haka kuma akwai Lateef Kayode Are (Amurka), Joseph Sola Iji (Rasha), Jimoh Ibrahim a matsayin wakilin dindindin na Nijeriya a Majalisar Dinkin Duniya, Isaak Adewole (Canada), Fatima Ajimobi (Austria), Lola Akande (Sweden), Ayodele Oke (Faransa) da Yakubu N. Gambo (Saudi Arabia).
Sauran sun hada da Nora Ladi Daduut (Koriya ta Kudu), Onueze Joe Okocha (Ireland), Kulu Haruna Abubakar (Tunisia) da Jerry Samuel Manwe (Trinidad and Tobago).
Sabbin jakadun na sa ran fara aiki a kasashen da aka tura su bayan kammala dukkan matakan diflomasiyya da suka dace.
