
Wasu ‘yan bindiga a Jihar Ribas, sun kai hari akan tawagar tsohon Ministan Sufuri, Chibuike Rotimi Amaechi bayan wasu da ake zargin ‘yan daba ne sun ƙone ofishin jam’iyyar adawa ta ADC a yankin.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ƙaramar hukumar Ikwerre a yau Juma’a, yayin da Amaechi ke kan hanyarsa ta zuwa garinsu na Ubima domin yin rajistar shiga jam’iyyar ADC ta hanyar tsarin e-registration.
Gabanin isowarsa, wasu da ake zargin ‘yan daba ne sun tare hanyoyi tare da hana wasu magoya bayan jam’iyyar ADC shiga garin domin halartar taron rajistar.
Rahotanni sun ce, a daren da ya gabata kafin aukuwar harin, wasu ‘yan bindiga sun kai hari tare da ƙona ofishin jam’iyyar ADC na mazaba a Ubima, sannan suka harba bindiga a yankin.
Lokacin da tawagar Amaechi ta yi ƙoƙarin shiga garin, ‘yan bindigar sun buɗe wuta kan ayarin motocin.
Sai dai jami’an tsaro da ke tare da shi sun mayar da martani, lamarin da ya sa maharan suka tsere zuwa cikin daji.
Bayan faruwar lamarin, Amaechi ya yaba wa jami’an tsaro — ciki har da ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro — bisa saurin da suka kai ɗauki, tare da kira ga hukumomi da su binciko tare da hukunta waɗanda ke da hannu a harin.
Ya kuma roƙi magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu tare da guje wa ɗaukar doka a hannunsu.
