Tinubu ya fasa halartar wasannin Legas kan iftila’in Anambara da Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya soke tafiya jiharsa ta Legas inda a nan ne ya saba yin hutu yayin bikin Kirismas, domin karrama waɗanda suka mutu a sakamakon turmutsutsin da ya janyo hasarar rayuka a Abuja da Jihar Anambra.

Mutane 10 ne suka mutu ciki har da ƙananan yara, inda da dama suka samu raunuku a wani turmutsutsu da ya faru a cocin Catholic dake Maitama a Abuja.

A wata sanarwa da rundunar ƴan sanda ta fitar a Abuja, ta ce cikin waɗanda suka mutu akwau ƙananan yara huɗu, yayin da mutum takwas suka samu munanan raunuka kuma suke karɓar magani a asibiti.

A Anambra kuwa rahotonni sun bayyana cewa wasu mutane sun mutu bayan wani turmutsutsu da aka samu a wajen rabon tallafi a jihar, a ranar ta Asabar.

Sanarwar da Fadar shugaban ƙasa ta fitar ta ce Shugaba Tinubu ya soke kallon wasan kwale-kwale da aka tsara zai yi a Ikoyi.

Ya kuma yi wa mamatan addu’a tare da fatan murmurewa ga waɗanda suka jikkata.

By Babaji